Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki

[ad_1]



A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki.

Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana.

Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna.

Jirgin zai ci gaba da zirga-zirga ne bayan kammala gyare-gyare da sauran tanade-tanaden kula da lafiya da tsaro bayan gocewar da ya yi daga kan layin dogo a ranar 26 ga watan Agusta, wanda ya yi sanadiyar tuntsurewar kusan ɗauƙacin taragoginsa.

Fasinjoji 22 ne aka tabbatar sun samu rauni daga cikin mutum 618 da ke cikin jirgin a lokacin da ya yi hatsarin. Babu asarar rayuka.

Kakakin Hukumar NRC, Callistus Unyimadu, ya ce, hukumar ta tuntuɓa tare da mayar wa mutum 512 daga cikin fasinjojin kuɗaɗensu.

Haka kuma ta tuntuɓi akasarin waɗanda suka jikkata inda ta ziyarci wasu gada cikinsu domin dubiya.

Ya ƙara da cewa hukumar ta tanadi kujera guda kyauta a duk mako ga duk fasinjojin da suka samu rauni a hatsarin, har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2025.

Ragowar fasinjojin jirgin da ya yi hatsarin kuma kowannensu zai samu kujera guda kyauta kafin ranar 31 ga watan Disamba, 2025.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *