Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar mutuwar mutane 58 sanadiyyar kamuwa da cutar amai da gudawa (kwalara) inda ta gano sabbin masu dauke da cutar mutane 258, wanda aka samu a kananan hukumomi 14 cikin 20 na jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Auwal Jatau ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da cutar kwalara na jiha, da kuma kwamitin kwararru kan yaki da cutar.

Jatau ya bukaci mambobin kwamitocin da su tunkari ayyukan da aka dora musu cikin kishi da kwarewa da kuma hanzari.

Mataimakin Gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin ya koka kan yadda cutar kwalara da ta sake barkewa, kuma tana ci gaba da janyo asarar rayuka, da kuma kawo cikas ga harkokin rayuwa da kuma kawo kalubalen ga tsarin kiwon lafiyar jihar.

Ya ce, cutar kwalara na daya daga cikin manyan cututtuka da ke barazana ga lafiyar al’umma, duk da kokarin da gwamnatin jihar da takwarorinta ke yi na shawo kan cutar.

Jatau ya bayyana cewa, kafa kwamitoci yana da mahimmanci wajen cimma manufofin da ake so.

“Ana iya yin rigakafin wadannan bullar cutar tare da daukar matakan da suka dace,, da kuma ci gaba da inganta tsaftar ruwan sha tsaftar muhalli, da tsaftar jiki.”

A kan haka ne ake sa ran kwamitin zai yi aiki tare da kungiyoyin hadin gwiwa don shawo kan matsalar.

Ya ce, Jihar Bauchi ta mayar da hankali kan barkewar cutar kwalara da kuma fitar da dabarun rigakafin cutar kwalara na dogon lokaci tare da tsare-tsare da tsare-tsare na kasa da kasa kan tsare-tsaren dakile cutar kwalara a Najeriya da yin rigakafi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *