An gudanar da gasar rubutun haruffa ta makarantun sakandare a Zariya

[ad_1]



An gudanar da gasar Rubutun Haruffan Kalmomi (Spelling Bee) ta makarantun sakandare karo na farko a garin Zariya, inda ɗalibai daga ƙananan aji (JSS) da manyan aji (SSS) daga Shiyya ta Ɗaya a Jihar Kaduna suka fafata wajen nuna bajinta da hazaƙar ilimi.

Gasar, wadda Team Addah ta shirya, ta gudana a Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, kuma ta samu gasa mai cike da ƙwazo, yayin da ɗalibai daga makarantu daban-daban suka fafata domin zama zakara.

An shirya gasar ne domin tallafa wa manufofin Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, na ƙara zuba jari a harkar ilimi, da nufin gano yara masu basira, bunƙasa tunaninsu da kuma samar musu da ingantaccen ilimi domin kyakkyawar makoma.

Da take jawabi a madadin gwamnan, Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da saka hannun jari a ilimin yara, tana mai cewa makomar kowace al’umma tana farawa ne daga kyakkyawar tarbiyya da ilimin yara.

Ta ce ilimi shi ne ginshiƙin samun makoma mai tabbaci, tare da tabbatar da ƙudurin gwamnati na samar da ilimi ga kowane yaro a faɗin jihar.

“Zuba jari a harkar ilimi shi ne babban abin da muke bai wa fifiko, domin samar da ilimi ƙofa ce ta zuba jarin zaman lafiya, ci gaba da wadata,” in ji ta.

Ta kuma yaba wa masu shirya gasar, wato Team Addah, da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar wajen ganin gasar ta yi nasara.

Haka nan, Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya bayyana gasar a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa tsarin ilimi a jihar, yana mai yaba wa masu shiryawa bisa jajircewa da sadaukarwa wajen bunƙasa ilimi.

Tun da fari, Mai Shirya Gasar Rubutun Haruffa, Barrista Aisha Ahmad Muhammad (Addah), ta ce an ƙirƙiri shirin ne domin tallafa wa shirin gyaran ilimi na gwamnatin jihar da kuma cike giɓin ƙoƙarin gwamnati wajen bunƙasa ƙwarewar ilimi a tsakanin ɗalibai.

Ta bayyana cewa makarantun sakandare daga ƙananan hukumomi takwas na Shiyya ta Ɗaya sun halarci gasar a rukunin ƙanana da manya, tana mai nuna jin daɗinta bisa irin hazaƙar da ɗaliban suka nuna.

A ƙarshen gasar, Zippora Victor daga Makarantar Sakandare ta Vital Years da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta zama zakara a rukunin manyan sakandare, yayin da Abdulaziz Alhassan daga Makarantar Sakandare ta Alu Dan Sidi da ke Ƙaramar Hukumar Zariya ya lashe rukunin ƙananan sakandare.

An bai wa zakarun gasar da sauran ɗaliban da suka halarta kuɗaɗen yabo da kyaututtukan ƙarfafawa.

Waɗanda suka yi alƙalancin gasar
Kyaututtuka da aka raba a ƙarshen gasar


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *