Shawarwarin Sin Sun Dace Da Yanayin Duniya
[ad_1]
A kwanan baya, firaministan kasar Serbia, Juro Macut, ya ziyarci kasar Sin, inda ya zanta da wakilin CMG a birnin Beijing. Yayin tattaunawar, Mista Macut, ya ce shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, da suka shafi gudanar da harkokin mulki a duniya, da kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, da dai sauransu, sun yi karin bayani kan ruhin kundin tsarin dokokin Majalisar Dinkin Duniya, kana nagartattun manufofi ne da suka dace da yanayin da duniyarmu ke ciki.
A cewar Mista Macut, duk wadannan shawarwari na Sin sun nuna ra’ayi na samun daidaito, inda ake neman sauraron ra’ayoyin dukkan kasashe daban daban, da mayar da hankali kan bukatar kasashe masu tasowa, yayin da a sa’i daya kuma ake lura da yanayin da kasashe masu sukuni ke ciki, don tabbatar da kafuwar al’ummar dan Adam mai makomar bai daya. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link