Zargin Almundahana: Kotu Ta Tisa Ƙeyar Malami Zuwa Gidan Yarin Kuje

[ad_1]

Wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami (SAN), a Gidan Yarin Kuje.

Mai shari’a Emeka Nwite ne, ya bayar da umarnin a ranar Talata, yayin da kotu ke jiran sauraron buƙatar belin Malami.

  • An Kashe Mutane 8 A Wasu Sabbin Hare-hare A Kebbi, ‘Yansanda Sun Fara Bincike
  • An Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu Kan Aiwatar Da Dokar Haraji

Haka kuma, kotun ta umarci a tsare ɗansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da wani wanda ake tuhuma tare da su, Bashir Asabe.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan sauraron hujjojin lauyoyin waɗanda ake tuhuma da na ɓangaren masu ƙara.

Malami da sauran waɗanda ake tuhuma na fuskantar tuhume-tuhume guda 16 na almundahanar kuɗaɗe da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar.

EFCC ta zarge su da haɗa kai wajen ɓoye da awon gaba da kuɗaɗe masu yawa tsawon shekaru.

Zarge-zargen sun haɗa da amfani da kamfanoni da asusun banki wajen yashe haramtattun kuɗaɗe da kuma sayen manyan kadarori a Abuja, Kano da sauran wurare.

Hukumar ta ƙara da cewa wasu daga cikin laifukan da ake zargi an aikata su ne a lokacin da Malami ke riƙe da mukamin Lauya na Ƙasa, abin da ya saɓa wa dokokin hana satar kuɗi na Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *