Nazarin CGTN: Matakin Amurka Na Kaddamar Da Yaki Zai Rage Karfinta Na Babakere
A lokacin da hare-haren Isra’ila da Amurka kan Iran suka koma kan kayayyakin samar da makamashi, yakin ya shiga wani sabon babi, inda Amurka ke gaggauta jefa kanta cikin tsaka mai wuya.
Wani nazarin jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta gudanar ta intanet ya nuna cewa, kaso 94.1 na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, hare-haren soji kan Iran, zai gaggauta raguwar karfin Amurka na babakere.
Cikin nazarin, kaso 90.9 na masu bayar da amsa sun ce hare-haren Amurka kan Iran na nuna dawowar ayyukan ta’addanci na Amurkar. Haka kuma, kaso 93.8 sun amince cewa, hare-haren kan Iran ba su halatta ba, kuma ba su da hujja. Har ila yau, kaso 89.1 na ganin matakin Amurka na kaddamar da yakin yunkuri ne na kare babakeren takardar kudi na dala da kuma sace albarkatun man Iran.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalolinta na harsunan Ingilishi da Sipaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda cikin sa’o’ 24, musu amfani da kafar intanet 18,906 suka bayyana ra’ayoyinsu. (FMM)