An Yi Taron Share Fage Na Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa A Addis Ababa

[ad_1]

A ranar 6 ga wata agogon wurin, an gudanar da “taron share fage na shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa mai lakabin “duniya na kallon shirin na CMG tare” a hedkwatar Kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa. Wannan taron na hadin gwiwa ne tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da Hukumar Kungiyar Tarayyar Afirka, da kuma Ofishin Jakadancin Sin a Tarayyar Afirka.

Shugaban Hukumar Kungiyar Tarayyar Afirka, Mahamoud Ali Youssouf, ya bayyana a cikin sakon taya murna cewa, a yau bikin bazara na kasar Sin ya wuce iyakokin kasa, ya kafa tushensa kuma ana yin murnarsa a sassa da dama na duniya. Ta hanyar muhimman dandaloli kamar na shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa, mutane daga ko ina cikin duniya na iya kallon al’adun Sinawa masu zurfi, da kuzari, da kuma yanayoyinsu masu ban sha’awa kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *