Indomie ta Gabatar Da Waƙoƙin Yabon Al’adu Na Farko Na Afirka Don Ranar Uwa ta duniya

[ad_1]



A wata rana mai cikin yanayi na zafi a wani falo a Legas, ‘yan’uwa su uku sun yi taɗi a waya, suna daidaita ƙarar wata waka da yanayin  murya mai ƙarfi ta cika sararin samaniya.

Waƙar ta yi kama da ta irin tada, waƙa, cikin girmamawa. Duk da haka babu wani mawaƙin yabon da ya shigo ɗakin.

Waƙoƙin yabon sun samo asali ne tun da daɗewa ta hanyar basirar wucin gadi.

Cikin daƙiƙoki kaɗan, sunan mahaifiyarsu ta shiga cikin waƙar da ke yawo tana murna a matsayin mai renon yara, mai karevginshiƙin iyalinta.

Ta ɗago kai cikin mamaki, tana dariya a hankali yayin da yabon ya ci gaba.

Abin da ya fara  cikin farin ciki mai natsuwa ga ‘ya’yanta, da nufin ya zama abin mamaki.

A gare ta, hakan ya yi kama da wanda aka saba da shi ba zato ba tsammani, kamar waƙoƙin yabon da ta ji suna mata.

A cikin ƙasar da aka daɗe ana girmama iyaye mata a cikin karin magana, waƙoƙin yabon tun kafin a fara nuna yabo a kafofin sada zumunta, wani sabon kamfen ne na Indomie Kuma  ƙoƙari ne  mai ban mamaki, dake haɗa basirar da hulɗar ɗan adam don yin magana da harshe na al’ada.

A cikin shirinta na Show Some Love To Mum na shekarar 2026, kamfanin taliya indomie  ya gabatar da abin da ya bayyana a matsayin dandamalin yabon al’adu na farko da ke amfani da fasahar AI a Najeriya. Dandalin yana bawa ‘yan Najeriya damar samar da waƙoƙin yabon jama’a na musamman da aka keɓe ga iyaye, don tabbatar da yada al’adun  da bada labari na asali.

Akwai fahimta mai sauƙi da godiya  mai tasiri sosai idan aka bayyana ta hanyar al’adu da aka saba.

A faɗin Afirka, girmama uwaye ya daɗe yana ɗaukar siffar waka.

A tsakanin Yarabawa, al’adar Oríkì tana  yabon kyawawan halaye, da gadon kakanninsu.

Sau da yawa ana kwatanta uwaye a matsayin  zinariya – kuma a matsayin masu kula da tunawa da iyali.

A cikin al’ummomin Igbo, karin magana kamar “Nne bu ndu,” ma’ana uwa ita ce rai, tana ɗaukar zurfin girmamawa ga uwa, yayin da waƙoƙin biki ke girmama mata a matsayin ginshiƙan motsin rai na gida.

A Arewacin Najeriya, mawaƙan yabon da ke yin Wakar yabo sun daɗe suna yabon mata a matsayin uwar gida, ginshiƙin gida.

Tun kafin a fara amfani da hashtags da jadawalin dijital, waɗannan al’adu sun kasance a matsayin bayyana godiya.

Indomie ta yi ƙoƙarin fassara wannan harshe zuwa zamanance don dacewa da aladunmu.

Ta hanyar wani dandamali na musamman, masu amfani suna nuna hotunan mahaifiyarsu, suna shigar da sunanta, suna zaɓar harshen al’ada kuma nan take suna karɓar bidiyon waƙoƙin yabo na musamman wanda aka yi wahayi zuwa gare su daga harshen Yorubanci da  Oríkì, waƙoƙin bikin na Igbo, Dana al’adun waƙoƙin Arewa, da kuma yabo a cikin harshen Ingilishi matakai ne na nuna kauna ga uwa..

Fasahar zamani, wacce za a iya saukewa na tsawon wata ɗaya ta  yanar gizo a wannan adireshi www.indomie.ng/showsomelovetomum, tana haɗa fasaha da ƙirƙirar ƙwaƙwalwa, tana sanya wani matsayin sabon abu don ci gaban  al’adu.

jingina ga haɗin kai na iyali, wani shiri ne dake wakiltar juyin halitta da inganta al’adu.

Ranar Uwa da AI ta fara ya sami karɓuwa da kyaututtuka, da bayyana abin da shugabannin kamfanoni suka bayyana a matsayin martani mai ƙarfi na habaka al’ada daga ‘yan Najeriya da ke sha’awar jin dadin waƙoƙin yabon uwa ta hanyoyin  zamani da na al’ada.

Sigar wannan shekara ta faɗaɗa wannan ra’ayin ta hanyar sanya al’adu,  a tsakiya don samun cigaban kasa.

A gidajen Najeriya, soyayya ba kasafai

take yin shiru ba; ana rera ta, ana magana da ita, kuma ana yaba mata,”

in ji Temitope Sule, Manajan Instant Noodles na Indomie.

Nuna Soyayya ga uwa, ba wai kawai muna amfani da AI a matsayin kayan aiki ba; muna koyar da fasaha don ciyar da al’ada gaba.

Lokacin da

kirkire-kirkire ke nuna asali, yana zama dole ga ɗan adam, kuma a nan ne haɗin kai na gaskiya ke rayuwa.

Da yake ba da ƙarin haske kan rawar da kamfen ɗin ya taka a birane, Ibrahim Isah, daga Legas, ya bayyana cewa shirin yana nuna yadda iyalai na zamani a Najeriya ke fuskantar al’adu a wurare na zamani ba tare da rasa zurfin motsin rai ba.

Jihar Lagos tana wakiltar wurin haɗuwa da raya al’adu da kirkire-kirkire.

Abin da muke gani shine matasan ‘yan Najeriya suna son bikin uwayensu ta hanyoyin da suke jin zamani amma har yanzu suna da tushe a cikin asali,” in ji shi.

Wannan dandamali yana ba da damar al’adu su yi tafiya a cikin saurin fasaha yayin da suke kiyaye sharudda da ake dasu

Lokacin da mutane suka ji sunan mahaifiyarsu da aka saka a cikin waƙoƙin yabo, yana daina zama talla kuma ya zama lokacin sirri.”

Masu lura da tallace tallace sun ce kamfen ɗin yana nuna babban sauyi a cikin ba da labarin kyakkyawar alama.

Maimakon watsa saƙonni, kirkire ƙirƙire akwai masu haɗin gwiwa inda masu sauraro ke taimakawa wajen samar da ma’ana da ake bukata.

Ga Ebere, Manajan Yankin, Kudu maso Yamma, wannan shiri ya yi tasiri sosai ga al’adun gargajiya na yabo da bayar da labarai da suka daɗe a cikin tsarin zamantakewa na

À yankinmu.

“Musamman a Kudu maso Yamma, waƙoƙin yabo sun fi aiki da tuna baya.

A Kudu maso Yamma, waƙoƙin yabo sun fi aiki da girmamawa, da kuma bayar da labarai tsakanin tsararraki,”

in ji ta. “Abin da Indomie ta yi shi ne sake fassara wannan al’adar ga iyalai na yau, ta tabbatar da cewa ko da a zamanin dijital, yara za su iya magana da harshen godiya da iyayensu suka fahimta ta hanyar da ba ta dace ba.”

A zamanin da basira ke bada gagarumin cigaba galibi ana danganta ta da sarrafa kanta da inganci da gwajin Indomie ya nuna wata dama ta fasaha a matsayin mai kula da al’adu maimakon maye gurbinta.

Ta hanyar mayar da algorithms zuwa mawaƙan yabo da wayoyin komai da ruwanka zuwa tasoshin gado, Nuna kauna ga uwa ya sake tsara kirkire-kirkire ba a matsayin rikici ba amma a matsayin ci gaba –

ƙungiyar mawaƙa ta zamani da ke ɗauke da ɗaya daga cikin tsoffin saƙonnin godiya na Afirka da girmamawa ga mahaifiyarka abune na farinciki.

KARSHE


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *