ADC Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Saki El-Rufai Ko Ta Gurfanar Da Shi A Kotu
[ad_1]
Jam’iyyar ADC ta buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta saki Nasir El-Rufai nan take ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da ɓata lokaci ba.
A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce tsare shi ba tare da shari’a ba ya saɓa wa doka kuma yana barazana ga dimokuraɗiyya.
- Ministan Harkokin Wajen Sin: Babakere Ba Ya Samar Da Mafita
- CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025
ADC ta kuma soki gwamnatin Bola Tinubu, tana mai cewa lamarin na haifar da tambayoyi kan mutunta haƙƙin ɗan Adam da bin doka.
Jam’iyyar ta jaddada cewa ‘yanci haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya tanada, ba wani abu ba ne da gwamnati ke bayarwa ko karɓa yadda ta ga dama ba.
Haka kuma ta buƙaci gwamnati da jami’an da abin ya shafa, ciki har da Nuhu Ribadu, da su bi doka tare da mutunta haƙƙin ‘yan ƙasa.
[ad_2]
Source link