Babu barazanar tsaro duk da jita-jitar harin ’yan bindiga — FUK




Hukumar Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK) a Jihar Gombe, ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa ’yan bindiga sun kai hari cikin jami’ar.

Jami’ar ta ce labarin ƙarya ne, kuma an ƙirƙire shi ne domin tayar da hankalin ɗalibai, iyaye da jama’a, tare da ƙoƙarin kawo cikas ga jarabawar zangon farko da ke gudana.

Babbar Jami’ar Yaɗa Labarai ta FUK, Janet Ibrahim Ezekiel, ta bayyana cewa babu wata barazanar tsaro a jami’ar.

“Shugabancin gdanarwar jami’a na jaddada cewa babu wani harin da aka kai a Jami’ar Tarayya ta Kashere. Wannan labari ƙarya ne da aka ƙirƙira domin haddasa firgici da ruɗani,” in ji sanarwar.

Ta ce abin da ya faru a zahiri rikici ne tsakanin wasu matasa daga garuruwan Jauro Buba da Garin Rigiya, waɗanda ke wajen harabar jami’ar.

Jami’ar ta ƙara da cewa rundunar ’yan sandan jihar ta shiga tsakani kuma ta shawo kan lamarin, inda aka dawo da zaman lafiya.

Jami’ar ta tabbatar wa iyaye da al’umma cewa babu wani abun tashin hankali domin akwai tsaro a cikin jami’ar.

Ta shawarci jama’a da su kasance masu neman sahihan hanyoyin sadarwar jami’a.

“Jami’ar Tarayya ta Kashere na ci gaba da ba da muhimmanci ga lafiyar ma’aikata da ɗalibai, kuma babu wata barazana ga harkokin karatu,” in ji sanarwar.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *