Ana shirin sako ’yan bindiga, sun kai sabbin hare-hare a Kastina
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai sababbin hare-hare a Jihar Katsina a yayin da gwamnatin jihar ke shirin sako wasu daga cikinsu da ke tsare a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin.
A ranar Lahadi da dare ne ’yan bindiga suka kai hari kan jerin gwanon motocin mahalarta ɗaurin aure, tare da kashe aƙalla mutane biyu tare da sace wasu 17, ciki har da amaryar, a yankin Unguwar Nagunda da ke ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta jihar.
Daga bisani mutum 8 daga cikin waɗanda aka sace sun tsere inda suka koma wurin iyalansu a ranar Litinin.
Kazalika ’yan bindiga sun kashe wani mutum a ƙauyen Kafa da ke kan babbar hanyae Kankara– Sheme da ka ƙaramar hukumar.
An kai waɗannan hare-haren wane washegarin da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Muazu, ya bayyana dalilan gwamnatin jihar a shirinta na sakin wasu mutane 70 da ke tsare kan ayyukan ta’addanci a jihar.
A hirarsa da kafar yada labarai ta DLC Hausa, Kwamishinan ya bayyana cewa mutanen da ake shirin sakowa suna fuskantar shari’a ne bisa tuhumar su da aika laifuka masu alaƙa da ayyukan ’yan bindiga.
A cewarsa, za a sake su ne domin ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomi suka kula da ƙungiyoyin ’yan bindiga a sassan jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link