Aikin tsaron cikin gida ba na sojoji ba ne — Buratai

[ad_1]



Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Buratai (murabus) ya yi gargaɗi kan dogaro da sojoji wajen ayyukan tsaron cikin gida.

Buratai ya soki yadda ake ta amfani da sojoji wajen tsaron cikin gida, da cewa hakan na raunana karfin ’yan sanda da kuma takura rundunar soji.

Ya bayyana cewa yawan tura sojoji a fadin jihohi 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya na rage ingancin ’yan sanda da hukumomin leken asiri da ya kamata su jagoranci harkokin tsaron cikin gida.

“Yawan tura sojojin Najeriya wajen tsaron cikin gida na kawo daidaito na gaggawa, amma yana haifar da dogaro da ke raunana karfin ’yan sanda da kuma takura matakan tsaro,” in ji Buratai.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a Kwalejin Tsaron Qasa da ke Abuja yayin taron tunawa da sojojin da suka mutu.

Ya ce karkatar da kasafin tsaro zuwa ayyukan ’yan sanda na yau da kullum ya sa rundunar sojoji ta yi nauyi, kuma hakan na rage shirin kare qasar daga barazanar waje. Ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya tanadi cewa sojoji su kare kasa daga hare-haren waje, su kare iyakoki, su murkushe tayar da kayar baya, tare da taimaka wa hukumomin farar hula idan bukata ta taso.

Buratai ya bukaci a samar da tsari na lokaci da sharudda da zai mayar da nauyin tsaron cikin gida ga hukumomin farar hula, yana mai cewa dorewar tsaro da dimokuradiyya na dogaro da karfin ’yan sanda da hukumomin leken asiri.

Tun da farko a jawabinsa, Ministan Tsaro kuma tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (murabus), ya bukaci a hada kai wajen dakile hanyoyin da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen safarar makamai, miyagun kwayoyi da sauran haramtattun kayayyaki ta hanyar sufuri na cikin gida.

Ya ce tsaro ba na sojoji kadai ba ne, ya shafi gwamnoni, sarakuna, shugabannin addini da al’umma baki daya.

“Tsaro hakkin kowa ne,” in ji Musa. “Dole mu hada kai don dakile hanyoyin da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen safarar makamai da miyagun kwayoyi.”

Janar Christopher Musa ya kara da cewa gwamnati na kokarin inganta jin dadin sojoji, horaswa da kuma samar da kayan tsaro a cikin gida domin rage dogaro da kasashen waje da kuma samar da ayyukan yi.

Ya yaba wa hafsoshin tsaro da dakarun Najeriya bisa jajircewa da sadaukarwarsu, yana mai cewa karin ayyukan rundunar sojin ruwa sun rage laifukan teku, sun kare muhimman kadarorin kasa, tare da karfafa samar da albarkatun man fetur a bakin teku.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *