’Yansanda Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Ƙauyen Kaduna
[ad_1]
’Yansanda a Jihar Kaduna sun daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Idissu da ke Ƙaramar Hukumar Giwa.
Sun kashe ’yan bindiga biyu, sannan sun ƙwato makamai.
- Xabi Alonso Ya Ajiye Aiki A Real Madrid Bayan Cimma Matsaya
- Sin Da EU Sun Amince Da Batun Kayyade Farashin Motoci Masu Amfani Lantarki Na Kasar Sin
’Yansanda sun ce maharan sun kai harin ne bayan mutanen ƙauyen sun ƙi biyan harajin da wani shugaban ’yan bindiga, Kachalla Sanusi Bajira, ya tilasta musu biya.
Bayan samun sahihan bayanai, ’yansanda tare da ’yan sa-kai sun garzaya ƙauyen, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.
A yayin artabun, an kashe ’yan bindiga biyu, yayin da sauran suka tsere zuwa daji.
An ƙwato bindigogi biyu da harsasai biyar.
Kwamishinan ’yansandan Jihar ya yaba da jajircewa da ƙwarewar jami’an, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da yaƙi da ’yan bindiga da sauran laifuka a jihar.
[ad_2]
Source link