Kotu ta wanke Abba Kyari kan wasu zarge-zarge
[ad_1]
Babbar kotun tarayyar Najeriya ta sallami dakataccen mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, ta kuma wanke shi daga wasu zarge-zarge 23 da ake yi masa.
A yayin da yake yanke hukuncin Mai shari’a James Omotosho kan zarge-zarge 23 da ake masa da suka shafi rashin bayyana kadarorinsa da Hukumar Hana sha da fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (NDLEA) ta shigar a kan Abba Kyari.
An gurfanar da DCP Abba Kyari tare da wasu ‘yan’uwansa biyu, Mohammed Kyari da Ali Kyari, wadanda ake zargi da yin rantsuwar karya da nufin boye asalin wasu kadarori da aka ce suna da alaƙa da jami’in ɗan sandan.
Sai dai, Alƙali Omotosho ya yanke hukuncin cewa hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyin ba ta gabatar da gamsassun shaidu da za su tabbatar da cewa kadarorin da aka ambata a cikin tuhumar mallakar Kyari ne ba.
A cewar alƙalin, dole ne a tabbatar da mallakar filaye ko gidaje ta hanyoyi sanannu kamar tarihin gargajiya, ingantattun takardun mallaka, shaidar zama a filin, ko kuma ikon mallaka da aka sani.
Ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun gaza gabatar da ko ɗaya daga cikin waɗannan nau’ikan shaidun don nuna cewa wani gida da ke rukunin gidaje na Fountain Estate, Kasana — wanda aka ce na Ramatu Kyari ne — mallakar dakatarren jami’in ɗan sandan ne.
Kotun ta kuma ce NDLEA ba ta gabatar da ƙwararan shaidun da suka haɗa Kyari da sauran kadarorin da aka ambata a cikin tuhumar ba, ciki har da gine-gine da ke kan hanyar Linda Choko a Asokoro, Abuja, da kuma wata kadarar da ke Maiduguri, Jihar Borno.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link