Mene Ne Sirrin Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin?
[ad_1]
Aminanmu ’yan Afirka da yawa suna mamakin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, kuma sun sha tambaya cewa mene ne sirrin kasar wajen kiyaye ci gabanta? A ganina, Emmanuel Matambo, darektan cibiyar nazarin harkokin Afirka da kasar Sin da ke jami’ar Johannesburg ta kasar Afirka ta Kudu, ya ba da amsar tambayar daga wani muhimmin fanni, idan muka yi la’akari da furucin da ya yi ba da jimawa ba, inda ya ce, “Wani muhimmin dalilin da ya sa kasar Sin ta ke zama ginshikin bunkasar tattalin arzikin duniya, shi ne yadda take dukufa a kan samar da sabon karfin da ke tabbatar da ci gabanta”, kuma a hakika muna iya gano hakan daga rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar a yau.
Da safiyar yau Alhamis aka kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wadda ta kasance hukumar koli ta kasar, inda a madadin majalisar gudanarwar kasar, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati, rahoton da ya shaida cewa, a shekarar 2025, kasar Sin ta yi ta raya sabon karfin samar da ci gabanta yadda ya kamata, kuma ta cimma gagaruman nasarori wajen kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, inda ta shiga sahun gaba ta fannonin nazarin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da harhada magunguna, da mutum-mutumin inji da kimiyyar “quantum” da sauransu.
“Sabon karfin da ke samar da ci gaban kasa” na nufin karfin da ake iya samu ta fannin bunkasa tattalin arziki ta hanyar hada fasahohin ci gaba da kuma sana’o’in gargajiya. A shagalin murnar bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin(CMG) ya gabatar a kwanan baya, shirin yadda mutum-mutumin inji kirar kasar Sin ke wasan Kungfu ya burge masu kallo daga duk fadin duniya, wanda ya shaida babban ci gaban kasar ta fannin kimiyya da fasaha, musamman ma sabon karfin da ke iya samar da ci gaba a kasar.
Ci gaban kimiyya da fasaha ba ya iya rabuwa da muhimmancin da gwamnati ta dora a fannin da ma tsare-tsaren da ta yi. A hakika, kullum kasar Sin na dora matukar muhimmanci a kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, idan mun yi la’akari da shirye-shiryenta na raya kasa na shekaru biyar biyar. Har wa yau, a shekarar 2025, kudaden da kasar Sin ta zuba ta fannin gudanar da ayyukan nazarin kimiyya da fasaha ya kai kudin Sin yuan triliyan 3 da biliyan 926. Idan kuma mun duba lokacin da aka aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, za mu gano cewa, yawan kudaden da aka zuba ya kiyaye matsakaicin karuwa da ya kai kaso 10% a kowace shekara.
A bana ne za a fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, kuma rahoton aikin gwamnati da aka gabatar a yau ya yi nuni da cewa, bisa ga daftarin shirin, kasar Sin za ta mai da hankali a kan tsayawa a kan kafafuwanta wajen raya kimiyya da fasaha, tare da inganta kirkire-kirkire da nazarin muhimman fasahohi na zamani, don ingiza gine-ginen kasar Sin na dijital, tare da fatan ganin karuwar kudin muhimman sana’o’i masu alaka da tattalin arziki na dijital ya kai kimanin kaso 12.5% na karuwar mizanin GDP na kasar baki daya.
Har ila yau, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ya riga ya zama wani muhimmin bangare na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Yadda kasar Sin za ta mai da hankalinta a kan raya sabon karfin samar da ci gabanta a yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, zai kuma haifar da damammaki ga kasashen Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa a fadin duniya. Kamar yadda wakilin gidan talabijin na QTV na kasar Gambia, Ousman Jatta, wanda a halin yanzu ke ba da rahotannin taron da ke gudana a Beijing ya ce, “Kasar Sin na taimakawa kasashe masu tasowa wajen tabbatar da ci gabansu. Kasar Sin ta kasance mai kishin zaman lafiya, kuma tana kokarin bunkasa fasahohi, yanzu haka a kasar Sin, motocin lantarki da fasahar AI sun zama ruwan dare. A kasarmu kuma, an zamanantar da hidimomin motocin haya na Taxi zuwa salon dijital, haka kuma ana kokarin zamanantar da harkokin motocin lantarki zuwa salon na dijital. Ana aiwatar da gyare-gyare, duk da cewa ba cikin sauri ba. Muna sa ran mu ma za mu iya cimma burin raya kanmu kamar yadda kasar Sin ta yi.” Alal hakika, furucinsa ya bayyana burin kasashen Afirka da dama, wato yadda kasar Sin ke kokarin zamanantar da kanta, na samar da abin koyi, da kuma damar hadin gwiwa ga kasashen Afirka a kokarinsu na zamanantar da kansu.
[ad_2]
Source link