Yadda Manyan Taruka Biyu Na Sin Ke Zamowa Madubin Turbar Ci Gaban Kasar

[ad_1]

Yayin da aka kaddamar da zama na hudu na majalisar wakilan jamaar kasar Sin wato NPC karo na 14, hankulan al’ummun kasa da kasa na kara karkata ga muhimman taruka biyu da kasar za ta gudanar cikin kwanaki masu zuwa, inda masharhanta da dama ke kallon taron shekara-shekara na majalisar wakilan jamaar Sin NPC, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC, a matsayin wata muhimmiyar dama ta kara fahimtar salon kasar Sin na siyasa da bunkasa tattalin arziki.

Manyan tarukan biyu suna kuma kara samar da wata muhimmiyar taga ta nazarin tsarin gudanar da gwamnatin Sin, da yadda kasar ke shigar da bukatun rayuwa, da zamantakewar al’ummunta su sama da biliyan 1.4 cikin managarcin tsarin tafiyar da mulki, da ma yadda ake shigar da ra’ayoyi masu fadi na al’ummun kasar cikin manufofin siyasar kasa da kudurorin da ake aiwatarwa a gwamnatance.

A duniyar yau, fahimtar ainihin ma’anar dimokaradiyya ba abu ne mai sauki ba. Amma duk da haka, mun san cewa dimokaradiyya ba wani abun ado ba ne da ake kafafa da shi, maimakon haka, turba ce ta warware matsalolin al’umma, wadda ake iya ganin ingancinta daga yadda rayuwar jama’a ke kara kyautata, da yadda manufofin gwamnati ke iya biyan bukatun al’umma yadda ya kamata. Idan har dimokaradiyya ta gaza yin haka, to ta zama surutai da hayaniya kawai!

Masharhanta da dama na kallon manyan tarukan nan biyu, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jamaar Sin NPC da na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC, a matsayin kyakkyawan misali na sahihiyar dimokaradiyya mai sauke nuyin dake wuyanta yadda ya kamata, kuma wadda ke zama misali mai kima ga sauran sassan duniya.

Muhimmin bambanci dangane da dimokaradiyyar kasar Sin da ta wasu sassan duniya, shi ne yadda ta kasar Sin ke raja’a kaco-kan wajen warware matsaloli na zahiri a matsayin aikin dake gaban komai, da tabbatar da ra’ayoyin al’umma sun taka rawar gani a fannin tsara manufofi, maimakon fakewa da dimokaradiyya wajen aiwatar da ra’ayoyin wasu tsirarun ’yan jari hujja!(Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *