Jihohin Nijeriya 5 Da Matsalar Tsaro Ta Fi Ƙamari A 2025 — Rahoto

[ad_1]

Matsalar tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan Nijeriya, inda hare-haren ’yan bindiga, masu iƙirarin jihadi, sace-sacen mutane da rikicin manoma da makiyaya ke haddasa asarar rayuka da dukiya.

Rahoton shekara-shekara da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited kasuwar kasuwa ya fitar, ya nuna cewa duk da ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a 2025, an samu ɗan ragi game da kashe-kashe da sace mutane idan aka kwatanta da 2024.

  • Xabi Alonso Ya Ajiye Aiki A Real Madrid Bayan Cimma Matsaya
  • Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Dalilin Sakin Mutane 70 Da Ake Zargi Da Ta’addanci

Rahoton ya yi la’akari da manyan laifuka biyu; kisan mutane da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa wajen tantance jihohin da suka fi fuskantar matsalar tsaro.

Jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a 2025 sun haɗa da Zamfara, wadda ta fi yawan sace mutane da kashe-kashe; Katsina fama da hare-haren ’yan bindiga; Neja, inda aka samu sace-sacen ɗalibai; Borno, cibiyar hare-haren Boko Haram da ISWAP; da Sakkwato wadda ke fama da hare-haren ’yan bindiga da na ’yan fashin daji.

Rahoton ya kuma nuna ɓullar matsalar tsaro a wasu jihohi da ba a saba gani ba kamar Kano, Kebbi da Kwara, inda aka samu hare-hare da sace-sacen mutane a wasu yankuna.

Duk da haka, Beacon Security ya ce an samu sauƙi kaɗan a yanayin tsaro gaba ɗaya a 2025 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *