Yadda Ake Samun Biliyoyin Daloli A Noman Zogale Da Kantu A Tekun Chadi
Shirin samar da abinci na duniya (WFP), ya yi nuni da cewa; za a iya samun kudaden shiga na kimanin biliyoyin daloli a noman Zogale da Kantu a Tekun Chadi, matukar an kara inganta tsaro da zaman lafiya a wannan kasa.
Mai wakiltar shirin a Nijeriya, Dabid Stebeson ya bayyana hakan ne a taron da aka yi karo na biyar na kungiyar gwamnonin yankin Tekun Chadi da aka gudanar a garin Maiduguri na Jihar Borno.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Yanayin Bazara” A Brazil
- Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho
“Yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci ta Afirka (AfCFTA), ta bayar da damar bunkasa hada-hadar kasuwanci tare da farfado da tattalin arzikin kasar, idan har aka bunkasa fannin aikin noma da kiwo.”
Mai wakiltar shirin ya sanar da cewa, bisa hadin kai a yankin da kuma wanzar da kuduri irin na siyasa, yankin zai iya magance kalubalen rashin abincin da za a ciyar da al’ummar da ke yankin.
Sai dai, Stebeson ya nuna takaicinsa kan cewa; duk da yawan sama da mutane miliyan bakwai da ke yankin, har yanzi al’ummar yankin na ci gaba da zama cikin karancin abinci.
A cewarsa, sama da mutane miliyan uku rikice-rikicen ta’addanci ya tilasta wa yin kaura daga matsugunansu.
Har ila yau, ya shawarci kungiyoyin da ke yankin; kan bukatar yin hadin kai mai karfi da samar da tsare-tsaren da za su habaka aikin noma da kiwon Kifi a yankin.