Mutane 597 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Cikin Wata 1 — FRSC


Hukumar Tsaron Hanya ta Tarayya (FRSC) ta sanar da cewa, kimanin mutane 597 suka mutu a hatsarin hanya a lokacin tafiye-tafiyen karshen shekara wanda yawanci ake fara ɗaukar bayanai tsakanin 15 ga Disamba, 2025, da 15 ga Janairu, 2026.

FRSC ta kara da cewa, ta ceto kimanin mutane 2,792 da suka jikkata a hadurran hanya a cikin wannan lokacin, wanda hakan ke nuna kwazo da kai daukin gaggawa domin ceto rayuka na jami’an hukumar.

Mai magana da yawun hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, a Abuja.

A cewarsa: “Bitar da aka yi ta nuna samun karuwar hadurra a tsakanin 15 ga Disambar 2025 da 15 ga Janairun 2026 idan aka kwatanta da bayanan da ake da su a shekarar bara, (2024/2025). Jimillar hadurran ababen hawa a kan hanya ya karu daga 665 a 2024/2025 zuwa 687 a 2025/2026.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *