Kokarin Zamanantar Da Sin Da Kasashen Afirka Bisa Hadin Gwiwar Raya Ayyukan Gona Na Zamani

[ad_1]

An sake samun girbi mai armashi a kasar Sin! Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar a kwanan nan sun nuna cewa, a shekarar 2025 da ta gabata, yawan hatsin da aka girbe a kasar ya kai tan miliyan 714 da dubu 880, wanda ya karu da kaso 1.2% bisa shekarar da ta gabace ta. Shekaru biyu a jere ke nan kasar Sin ta kai ga girbe hatsi sama da ton miliyan 700.

Hakan ya faru ne sakamakon yadda kasar Sin take matukar dora muhimmanci a kan raya noma da karkara da kuma manoma, wanda kuma ya samu shaida daga “kundinta mai lamba ta farko” da ta kan bayar a farkon kowace shekara. Kasancewarsa kundin gwamnati da ya shafi manufofinta, kundin ya yi ta nuna alkiblar da za a bi wajen raya abubuwan da suka shafi noma da karkara da kuma manoma. A jiya Talata, kasar Sin ta fitar da  “kundinta mai lamba ta farko” na shekarar 2026, inda ta bayyana tsare-tsaren bunkasa zamanantar da noma da yankunan karkara da kuma inganta raya karkara a dukkan fannoni. Tun daga shekarun 1980 zuwa yanzu, shekaru sama da 40 a jere ke nan, kundin mai lamba ta farko da kasar Sin ta bayar yake daukar jigon da ya shafi noma da karkara da kuma manoma, matakin da ya shaida muhimmancin ayyukan raya noma da karkara da kuma manoma ga kasar Sin.

Amma me ya sa kasar Sin ke dora matukar muhimmanci a kan raya noma da karkara da kuma manoma? Amsa ita ce sabo da kasar Sin kasa ce da ke da al’umma biliyan 1.4, kuma daga cikinsu kaso 1/3 manoma ne. Don haka, batun noma da karkara da kuma manoma, ba kawai yana shafar samar da isasshen abinci ga ‘yan kasar ba ne, hatta ma yana da alaka da zamanantarwar kasar baki daya.

Noma tushen arzki, abin hakan yake. A nahiyar Afirka, musamman kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, ayyukan noma kan dauki sama da kaso 30% daga cikin jimillar karfin tattalin arziki ta GDP, yayin da sama da kaso 70% na al’ummomin da suke da ayyukan yi suna gudanar da sana’o’i ne da suka shafi noma. Don haka ma, batun raya noma da karkara da kuma manoma su ma suna taka muhimmiyar rawa wurin daidaita matsalolin da kasashen suke fuskanta ta fannonin abinci da saukaka fatara da ma zamanantar da kansu.

Kasancewarta kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kullum kasar Sin na kallon kanta da kasashen Afirka a matsayin al’ummu mai makoma ta bai-daya, abin da ya sa take kokarin bayyana dabarunta da ma damammakinta ga kasashen Afirka a lokacin da take bunkasa kanta ta fannonin noma da karkara da ma manoma. A gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a shekarar 2024 a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu matakai 10 na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wajen zamanantar da kansu, ciki har da matakin da ya shafi bunkasa ayyukan noma, wato za a samar da gudummawar hatsi na kimanin kudin Sin yuan biliyan daya ga kasashen Afirka cikin gaggawa, da kafa yankunan nune-nunen fasahohin noma da tura masanan ayyukan noma 500 zuwa kasashen Afirka da kafa kawancen kirkire-kirkiren fasahohin noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka da dai sauransu.

In mun ba da misali da Nijeriya, cibiyar nune-nunen fasahohin noma da kasar Sin ta gina a kasar ta hada hannu da cibiyar nazarin fasahar noma ta kasar Sin da sauran cibiyoyin nazari wajen ayyukan inganta ire-iren shinkafa da rogo da gyada da sauran amfanin gona, kuma sabon nau’in shinkafar da ta kirkiro na iya samar da karin shinkafa na sama da kaso 20%, wanda har ya amfanar da manoma sama da dubu 200. A sa’i daya kuma, kamfanonin kasar Sin suna kokarin shiga ayyukan ban ruwa a kasar, wadanda har suka gina manyan tsarukan ban ruwa a jihohin Kano da Gombe da kuma Jigawa, wadanda suka shafi gonaki masu fadin eka dubu 22. Ban da haka, ta hanyar shirya kwasa-kwasai iri iri, kasar Sin ta taimaka wajen horar da dimbin kwararrun ayyukan gona ga Nijeriya.

Bana ta kasance shekarar da kasar Sin za ta fara aiwatar da shirinta na raya tattalin arziki da zaman al’umma na shekaru biyar biyar karo na 15, haka kuma wani sabon mafari ne a kokarinta na zamanantar da kanta. Kasancewarsu kawayen juna, kasar Sin za ta rika bayar da cin gajiyar nasarorinta ga aminanta na Afirka wajen zamanantar da ayyukan noma, don su cimma burinsu na zamanantar da kansu. (Lubabatu Lei)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *