2025: Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 12,446 a Kano — Hisbah
[ad_1]
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe guda 12,446 daga wajen jama’a a faɗin Ƙananan Hukumomin 44 na jihar a shekarar 2025.
Mataimakin Kwamandan hukumar, Dokta Mujahiddeen Aminuddeen ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce hukumar ta samu nasarar warware ƙorafe-ƙorafe 1,908 daga a hedkwatar hukumar da kuma ofisoshin Hisbah da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar.
A cewarsa, hukumar ta kuma taimaka wa mazauna jihar wajen ƙwato Naira 145.4 miliyan ta hanyar biyan bashi da tallafin yara.
Dokta Aminuddeen ya bayyana cewa, hukumar ta gudanar da manyan ayyuka guda tara a shekarar 2025.
Ya ce hukumar ta damƙe mutum 132 a wurare daban-daban a ciki da wajen Kano.
Hakazalika, ya ce hukumar ta naɗi bayanan laifuka 4,246 a hedikwatarta da ofisoshinta na ƙananan hukumomi, waɗanda daga bisani aka mika wa ’yan sanda da sauran hukumomi domin yin bincike da gurfanarwa a gaban kotu.
Mataimakin kwamandan ya yi kira ga ma’aikatun gwamnati, hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai da Hisbah domin rage ayyukan da suka saba wa dokokin Shari’ar Musulunci a jihar Kano.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link