Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe
[ad_1]
Kilishiyar Waja, Hajiya Rabee Abubakar Kulani, ta kai ziyara gidan gyaran hali na Gombe, inda ta raba mata fursunoni kayan tsaftar jiki domin su kula da kansu a lokacin al’ada.
Ta ce ta kai wannan gudummawa ne domin tallafa wa mata fursunoni wajen kare mutuncinsu, ganin cewa sau da yawa ba su da damar samun irin waɗannan muhimman kayayyaki.
“Ina so su ji kamar sauran mata, su samu tsafta da mutunci duk da yanayin da suke ciki.
“Shi ya sa na sayi kayayyakin da kaina domin na tallafa musu,” in ji ta.
A yayin ziyarar, ta kuma tattauna da su kan batun lafiya da haƙƙin haihuwa, tare da jaddada muhimmancin tsaftar al’ada.
Ta samu rakiyar Hajiya Hauwa Saraki, shugabar NCWS a Gombe, da kuma Hauwa Musa Babaji, mai fafutukar kare haƙƙin mata.
Sun yaba da yadda aka samu ci gaba wajen kula da jin daɗin fursunoni idan aka kwatanta da shekarun baya.
Shugaban gidan gyaran hali na Gombe, DCC Victor Odafen, ya gode mata bisa wannan tallafi.
Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyi da mutane masu hali su yi koyi da ita wajen tallafa wa fursunoni.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link