’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
[ad_1]
’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.
Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance.
Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku.
Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan.
Mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun isa ne a kan babura inda suka ajiye su daga nesa, sannan suka shiga ƙauyen a ƙafa.
A yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar kwanan nan, Gwamna Abba Yusuf, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro.
Ya kuma ce hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da ɓarayi shanu a wasu yankunan Arewacin jihar, babban abin damuwa ne.
Gwamnan, ya ce suna aiki tare da hukumomin tsaro don magance barazanar da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Ya bayyana ƙananan hukumomin da abin ya shafa; Kunchi, Tsanyawa, Gwarzo, Kabo, Sumaila, Shanono, Tudun Wada, Doguwa, da Rogo.
Amma ya ce hukumomi na ci gaba da ayyuka domin toshe hanyoyin shigowar ’yan bindiga da kuma kare al’ummomin ƙauyuka.
“Duk da wasu ƙalubale da ake fuskanta a nan da can, jama’a su kwantar da hankalinsu, gwamnati tana aiki domin magance duk wata barazana ga zaman lafiya,” in ji Yusuf.
Gwamnan, ya kuma goyi bayan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ayyana dokar ta-ɓaci a harkar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link