AFCON 2025: Hukumar CAF Ta Sauya Alƙalin Da Zai Jagoranci Wasan Nijeriya Da Algeria
[ad_1]
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) ta naɗa alƙalin wasa Issa Sy ɗan ƙasar Senegal domin ya jagoranci wasan daf da na kusa da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Afrika ta shekarar 2025 da za a buga yau Asabar tsakanin Nijeriya da Algeria a birnin Marrakech.
Tunda farko CAF ta naɗa Omar Artan a matsayin wanda zai yi alƙalanci a wasan, amma daga baya ta sauya shawara saboda fargabar da ake da ita game da yadda alƙalancin wasa ya taɓarɓare a gasar.
- AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Algeria A Wasan Kwata Fainal
- AFCON: Tunisia Ta Kori Kocinta Bayan Ficewa Daga Gasar
Issa Sy ba baƙon suna bane a gasar ta AFCON 2025, bayan ya yi aiki a matsayin mai kula da na’urar VAR a wasan rukuni tsakanin Morocco da Tanzania, ana sa ran naɗin Issa zai rage zarge-zargen da ake da shi dangane da alƙalanci a gasar, hakazalika ya kuma rage wasiwasin da magoya bayan ƙasashen biyu ke da shi na samun adalci yayin da Nijeriya da Algeria zasu fafata domin samun gurbi a wasan kusa da na ƙarshe.
Super Eagles ta kawo wannan matakin ba tare da rashin nasara ko ɗaya ba, inda ta lallasa ƙasar Mozambique a wasan zagayen 16 da ci 4-0, yayin da Algeria ta doke Dimokuraɗiyyar Congo da ci 1 mai ban haushi a wasan mintuna 120 da suka buga, wasan na ranar Asabar zai zama tamkar ɗaukar fansa a wajen Nijeriya, ƙasar dake Yammacin Afrika tayi rashin nasara a irin wannan matakin a hannun Algeria da ci 2-1 a shekarar 2019.
[ad_2]
Source link