Gwamnati Za Ta Tura Runduna Ta Musamman Jihar Kwara Da Neja
[ad_1]
Shugaban Hafsan Sojin Kasa (CDS), Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana shirin Babban Hedikwatar Tsaro (DHK) na tura Rundunar Hadin Gwiwar Musamman, wadda aka sanya wa lakabi da Operation Sabannah Shield, don kamo ‘yan ta’adda da ke aiki a Jihar Kwara da wasu sassan Jihar Neja dake makwabtaka.
Oluyede ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja, yayin zaman kasafin kudi na 2026 da Kwamitin Wakilai kan Tsaro ya shirya.
- Fubara Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Ribas
- Mu’amala Tsakanin Shugabannin Sin Da Amurka Tana Taka Muhimmiyar Rawa A Dangantakar Kasashen
Ya ce wannan aikin zai kunshi tura rundunonin musamman, inda za a sake tura wasu kayan aiki daga wasu wurare don karfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Ya bayyana cewa rundunonin musamman sun riga sun shiga Jihar Benuwe da Filato, yayin da ‘Operation Sabannah Shield’ za a kaddamar da ita nan ba da jimawa ba don magance barazanar tsaro a Kwara da wasu sassan Neja.
Yayin da yake bayyana ci gaban da Sojojin Nijeriya suka samu wajen raunana kungiyoyin ‘yan ta’adda da gungun fashi a fadin kasar, Oluyede ya jaddada bukatar gaggawa ta karfafa ‘Yan Sanda na Nijeriya (NPF) da Hukumar Tsaron Farar Hula (NSCDC) don tabbatar da dorewar nasarorin.
Ya yi bayani cewa, ko da yake sojoji sun yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda daga wurare da dama, dorewar zaman lafiya na bukatar samar da kayan aiki da isassun horo ga ‘yan sanda da jami’an tsaron farar hula, wadanda ke da yawan ma’aikata da kuma kusanci da al’umma sosai.
[ad_2]
Source link