An yi yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu a bara — DHQ
[ad_1]
Shalkwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da cewa an yi yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar da ta gabata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, wanda shi ne karo na farko da ta fito fili ta tabbatar da cewa an yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar.
A cikin sanarwar da Manjo Janar Sama’ila Uba ya rattaba hannu a kai, rundunar ta ce ta riga ta miƙa rahoton binciken ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar tsaron Najeriya ta ce ta kammala binciken yunƙurin juyin mulkin da aka yi a shekarar da ta gabata, tare da bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotun soji ta musamman.
“Rundunar tsaron Najeriya na sanar da al’umma cewa an kammala binciken yunƙurin juyin mulkin da aka yi. An gano jami’an soji 16 da suka aikata laifuka da suka saɓa da ƙa’idojin aikin soji, kuma an miƙa rahoton binciken zuwa mataki na gaba kamar yadda doka ta tanada,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya tabbatar da cewa an yi yunƙurin kifar da gwamnati, tare da bayyana cewa waɗanda aka samu da laifi za su bayyana a gaban kotun soji domin fuskantar shari’a kamar yadda kundin tsarin aikin soji ya tanada.
Tun a watan Oktoban 2025 ne rundunar tsaron ta sanar da kame wasu manyan jami’an soji 16 bisa zargin saɓa dokokin aikin soji, sai dai a wancan lokaci ta ƙi amsa zargin cewa an kame su ne saboda shirin juyin mulki.
A wancan lokaci, wata kafar labarai a Najeriya ta ruwaito cewa sashen tattara bayanan sirri na ƙasar ya kama jami’an sojin masu muƙamai daga kyaftin zuwa birgediya janar, yayin da ake zargin suna gudanar da wani taron sirri domin shirya kifar da gwamnati.
Rahoton ya kuma alaƙanta matakin soke faretin bikin cikar Najeriya shekara 1 ga watan Oktoba da wannan yunƙuri, sai dai kakakin shalkwatar tsaron a lokacin, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya yi watsi da zargin, yana mai cewa yunƙurin ne na haddasa rikice-rikice da tayar da hankalin jama’a.
Sai dai a ranar Litinin, yayin da yake ƙarin haske kan lamarin, kakakin rundunar tsaron, Manjo Janar Sama’ila Uba, ya ce bayan kammala dogon bincike na musamman da aka gudanar kan jami’an, an tabbatar da cewa suna kitsa shirin kifar da gwamnatin Najeriya.
A cewarsa, jami’an sojin 16 ɗin za su gurfana a gaban kotun soji domin amsa tuhuma bisa tanadin dokokin aikin sojin Najeriya, inda ya jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaskiya da adalci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link