Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce A Kamaru
[ad_1]
Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru.
Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci.
A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci gaban dangantakar Sin da Kamaru, kuma yana fatan hadin gwiwa da shugaba Paul Biya, don aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Beijing a bara, ta yadda za a inganta cikakkiyar alaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare masu zurfi, da kyautata rayuwar al’ummomin kasashen biyu. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link