Yanzu-yanzu: Burin Nijeriya Na Zuwa Gasar Kofin Duniya Ya Hadu Da Cikas
[ad_1]
Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta wargaza burin da babbar tawagar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles kedashi na buga gasar a shekarar 2026, yayinda ta tabbatar da kasar Dimokuradiyyar Congo a cikin kasashen da zasu buga wasannin share dage na gasar a watan Maris Mai kamawa.
Yau Laraba FIFA ta gabatar da jerin kasashen da zasu buga wasannin share fagen shiga gasar a watan Maris wanda za a buga a kasar Mexico, inda ta saka sunan Dimokuradiyyar Congo a matsayin wakilan nahiyar Afirka a wasannin, kasashen da zasu buga wasannin share fagen sun hada da Bolivia, Congo DR, Iraq, Jamaica, New Caledonia da Suriname.
Wannan matakin na FIFA ya wargaza fatan Nijeriya na samun damar zuwa gasar cin kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026, a cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, FIFA ta yi cikakken bayani game da tsarin gasar kuma ta lissafa kasashe shida da zasu buga wasannin share fagen shiga gasar.
Shigar Congo cikin jerin kasashen ya nuna cewar Nijeriya bata cikin kasashen, tunda farko hukumar kwallon Kafa ta Nijeriya ta shigar da kara a hukumance, tana zargin cewa Congo tayi amfani da yan wasan da Basu cancanta a wasan da kasashen biyu sukabuga a watan Nuwambar shekarar da ta gabata inda suka tashi da ci 1-1 kafin Congo ta fitar da Nijeriya a bugun Fenarati.
[ad_2]
Source link