Dalilin da ya sa na ƙi amsa tambayoyin ICPC — El-Rufai

[ad_1]



Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya ƙi amsa tambayoyin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta yi masa ne saboda yana ganin binciken da ake yi masa yarfe ne na siyasa.

El-Rufai yana tsare tun daga ranar 16 ga watan Fabrairu, bayan ya amsa gayyatar Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC).

Bayan sa’o’i 48, EFCC ta bayar da belinsa, amma nan take ICPC ta kama shi domin ci gaba da tsare shi.

A cikin martani guda biyu da ya bai wa jami’an ICPC, El-Rufai ya ce yana amfani da haƙƙinsa na kundin tsarin mulki na yin shiru.

Ya ce zai amsa duk zarge-zargen ne kawai a gaban kotu.

A bayaninsa, ya bayyana sunansa da tarihinsa.

Ya ce an haife shi a garin Dandawa, Jihar Katsina, a shekarar 1960, kuma ya taso tare da yin rayuwarsa a Jihar Kaduna.

Ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin Quantity Surveying.

Haka kuma ya yi karatu a jami’ar Harvard University da kuma University of London.

Ya lissafo muƙaman da ya riƙe a baya, ciki har da Darakta Janar na Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (1999–2003), Ministan Babban Birnin Tarayya (2003–2007), da kuma gwamnan Jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023.

Ya ce yanzu ya yi ritaya inda ya fi zama a ƙasar Masar tare da iyalinsa da mahaifiyarsa mai shekaru 96 a duniya.

El-Rufai ya ce shi babban jigo ne a jam’iyyar ADC, wadda ya bayyana ta a matsayin babbar jam’iyyar adawa.

Ya yi zargin cewa muƙaman da riƙe na siyasa ne dalilin da ya sa ake bincike a kansa.

Ya jaddada cewa, ba zai amsa wata tambaya ba kamar yadda lauyansa ya ba shi shawara.

Ya ce idan ICPC na da hujja a kansa, ta kai batun gaban kotu, inda zai kare kansa.

A gefe guda kuma, ɗansa Bello El-Rufai ya zargi ICPC da amfani da rashin amsa tambayoyin mahaifinsa, wajen cutar da shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *