Gwamnati ta dakatar da jigilar Kiristoci masu zuwa ibada Isra’ila saboda rikicin Gabas ta Tsakiya
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da dukkanin zirga-zirgar Kiristoci masu zuwa ibada Isra’ila sakamakon rikicin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya.
Hukumar Aikin Hajjin Kiristoci (NCPC) ce, ta sanar da wannan mataki a ranar Talata.
Babban Sakataren Hukumar, Bishop Stephen Adegbite, ya bayyana hakan a wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na hukumar ya fitar a Abuja.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kare ’yan Najeriya daga faɗa wa hatsari.
A cewarsa, abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da ayyana dokar ta-ɓaci a Isra’ila, sun sa ya zama dole a dakatar da dukkanin shirye-shiryen aikin Hajjin.
Dakatarwar ta shafi duka ayyukan hajjin da gwamnati ke tsarawa da kuma waɗanda kamfanoni masu zaman kansu ke gudanarwa.
Adegbite, ya ce hukumar na sa ido kan halin da ake ciki, tare da gode wa masu ruwa da tsaki da kafafen yaɗa labarai bisa haɗin kai da suke ba su.
Ya kuma roƙi ’yan Najeriya da su yi addu’ar samun zaman lafiya a Urushalima da ma yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.
A gefe guda, hukumar ta tabbatar da cewa an kammala aikin hajjin shekarar 2025 zuwa Isra’ila da Jordan cikin nasara.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link