Birtaniya ta fara shirye-shiryen tarbar Tinubu da mai ɗakinsa
[ad_1]
Hukumomi a ƙasar Birtaniya sun sanar da ɗaukar ƙwararan matakan tsaro, waɗanda suka haɗa da rufe hanyoyi na ɗan lokaci da kuma takaita zirga-zirga a sararin samaniya, gabannin ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ƙasar.
Ziyarar, wadda Sarki Charles na III zai karbi baƙuncinta, an shirya fara ta ne a ranar 18 ga watan Maris, inda ake sa ran shugaban Nijeriyar zai isa tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu domin gudanar da liyafar tarba a fadar Windsor Castle.
A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Thames ɓalley ta wallafa a shafinta na intanet, ta bayyana cewa tana haɗa gwiwa da hukumomin gundumar Royal Borough of Windsor da Maidenhead, da ma’aikatan fadar sarki, da sauran abokan hulɗa domin tsara dabarun tsaro kafin ziyarar.
’Yan sandan sun bayyana cewa, za a faɗaɗa takunkumin zirga-zirgar sararin samaniya da ke kan fadar Windsor Castle a ranar 18 ga Maris, tun daga ƙarfe 7 na safe zuwa ƙarfe 11:59 na dare, a matsayin ɓangare na shirye-shiryen tsaro.
Da yake ƙarin bayani kan shirye-shiryen, babban jami’in ’yan sanda Adrian Hall na sashin haɗin gwiwa na rundunar, ya ce waɗannan matakan wani ɓangare ne na babban shirin tsaro na ziyarar shugaban Najeriya Tinubu a mako mai zuwa.
“Takunkumin sararin samaniya ɓangare ɗaya ne kawai na ƙwararan matakan tsaronmu na ziyarar Shugaba Tinubu na Nijeriya a mako mai zuwa; akwai matakai da dama da za ku gani, wasu kuma ba za ku gani ba,” in ji Hall.
Ya ƙara da cewa: “A matsayinmu na runduna, muna da ƙwarewa sosai wajen tabbatar da tsaro a tarukan masarauta a Windsor, kuma an ɗauki lokaci mai tsawo ana tsare-tsare da shirye-shirye domin wannan taron.”
Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya karya dokar zirga-zirgar jiragen sama za a ɗauke shi a matsayin mai aikata laifi. “Za mu ɗauki tsauraran matakai wajen tabbatar da bin waɗannan dokoki; duk wanda ya karya su yana aikata laifi ne a ƙarƙashin dokar zirga-zirgar sararin samaniya kuma ana iya kama shi,” in ji shi.
A cewar Hall, aikin tsaron zai haɗa da jami’ai masu ƙwarewa na musamman, waɗanda suka haɗa da ƙungiyoyin bincike, ’yan sanda masu dawakai, sashin kula da zirga-zirgar hanyoyi, da jami’ai masu ɗauke da makami, tare da jami’an ‘yan sandan unguwa.
Hukumomin sun kuma shirya yin amfani da dukkan kyamarorin tsaro (CCTV) na Windsor da sauran dabarun kariya na zamani domin tabbatar da nasarar aikin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link