Tsarin 60/40: Ana Shirin Tankaɗe Da Rairaya A Majalisar Zartarwar Kano

[ad_1]

Alamu na nuna cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin yin babban sauyi a majalisar zartarwar jihar, inda ake sa ran za a yi amfani da tsarin rabon iko na kashi 60/40 wajen sake fasalin gwamnati. Majiyoyi a cikin gwamnati da jam’iyyar APC sun ce tattaunawa kan batun ya kai mataki na ƙarshe, musamman bayan sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar mai mulki.

Wata majiya ta ce an tsara tsarin ne domin daidaita tsarin gwamnati da sabon yanayin siyasa a jihar. A cewar majiyoyin, kashi 60 cikin ɗari na muƙaman siyasa za su tafi ga sabbin mambobin APC masu biyayya ga gwamnan, yayin da kashi 40 za su rage a hannun tsohon ɓangaren APC da ke da alaƙa da Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau Jibrin.

  • Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas
  • Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da  Biyan Biliyan 19 Don Ci Gaba da Aikin Titin Kano–Gwarzo–Dayi — Barau

Rahotanni sun nuna cewa tsarin zai shafi har ma da rabon iko a wasu ƙananan hukumomi, domin nuna daidaito tsakanin ɓangarorin biyu. Wani masanin siyasa a Kano, Malam Usman Balarabe, ya ce sauye-sauye irin wannan ba sabon abu ba ne bayan sauya sheƙa, musamman idan zaɓe na tafe.

Sauya sheƙar gwamnan zuwa APC ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da shugaban APC na ƙasa. Masu sa ido na ganin matakin a matsayin yunƙurin ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da daidaito a cikin jam’iyyar a Kano.

KanoTimes ta rawaito cewa; duk da cewa ba a fitar da jerin sunayen waɗanda sauyin zai shafa ba, majiyoyi sun ce ana sa ran wasu kwamishinoni da manyan muƙarraban gwamnati za su fuskanci sauyi, inda wasu za su ci gaba da zama, wasu kuma za a sauya musu wurin aiki domin dacewa da sabon tsarin siyasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *