An yi garkuwa da Fasto da wasu 4 a Jihar Kogi

[ad_1]



’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto na coci Living Faith Church da ke Okeoffin-Okoro Gbede, a Karamar Hukuamr Ijumu ta Jihar Kogi.

A cewar mazauna yankin, faston yana kan hanyarsa ta zuwa gona a kan babur na haya a ranar Asabar ne ya fada a tarkon ’yan bindigar.

An ce ya yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar tsalle daga kan babur din, amma ’yan ta’addan suka rinjaye shi, suka  yi awon gaba da shi, amma ma babur din ya tsere.

A ranar Lahadi kuma, ’yan bindigar suka kai hari a garin Odo-Ere, hedikwatar Karamar Hukumar Yagba ta Arewa, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna garin da ba a tabbatar da adadinsu ba tukuna.

Shaidu sun ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10 na dare, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, suna harbi a iska domin tsoratar da jama’a.

Wani mazaunin garin ya ƙara da cewa tun da safe an ga wasu baki da suka shigo garin suna ikirarin cewa ’yan gudun hijira ne daga wani hari a makwabtansu.

Sai dai jama’a sun nuna damuwa saboda babu jami’an gwamnati da suka yi rajista ko binciken shigowar su. Wasu na zargin cewa maharan na iya kasancewa cikin waɗanda suka shigo a matsayin ’yan gudun hijira.

Rahoton da aka samu daga garin a ranar Litinin ya tabbatar da cewa mutane hudu sun shiga hannun ’yan bindigar, ciki har da wata mata mai da maza uku.

Ana ci gaba da ƙididdiga domin gano adadin waɗanda aka sace ko kuma suka gudu domin tsira a wurare daban-daban.

Mazauna yankin sun ce suna rayuwa cikin tsoro tun bayan harin, inda wasu ke tunanin barin garin idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin gwamnati na jiha ko na ƙaramar hukuma. Koƙarin da aka yi na jin ta bakin mai magana da yawun gwamnati, Kingsley Fanwo, da kuma kakakin ’yan sandan jihar Kogi, CSP William Aya, bai yi nasara ba a lokacin da aka kammala rahoton.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *