Dakatar da Sheikh Alƙali Zariya kan sukar Tinubu ya tayar da ƙura
[ad_1]
Dakatar da malamin addinin Musulunci, Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zariya, da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jos ta yi, ya tayar da ƙura a kafafen sada zumunta.
An gayyaci Sheikh Alkali ne domin jagorantar Tafsirin Ramadan a Masallacin Mokas da ke Damaturu, a Jihar Yobe.
Daga baya an dakatar da shi bayan ya soki Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a lokacin da yake wa’azi.
Rahotanni sun ce dakatarwar ta biyo bayan wani taro da Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS na ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya kira.
Taron ya haɗa da malamin da shugabannin JIBWIS na jihar Yobe.
An zarge shi da amfani da kalamai masu tsauri kan wasu mutane a yankin da kuma kan shugaban ƙasa.
Ƙungiyar ta ce yadda ya yi magana kan matsalar tsaro bai yi daidai da tsarin da suka saba bi ba.
A cikin Tafsirinsa, Alƙali ya yi kakkausar suka kan rashawa da matsalar tsaro.
Ya soki wasu gwamnonin Arewa maso Yamma da Shugaba Tinubu, yana mai cewa ba su ƙoƙari wajen kawo ƙarshen satar mutane da hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Alƙali ya ce, “A yau ana sace mutane ana sayar da su kamar shanu. Ana ɗaukar mutum a kai shi daji, sannan a fara ciniki kan kuɗin fansa.
“Magidanta suna roƙon a tausaya musu, duk da cewa masu garkuwar jahilai ne. Suna duka da tattaka waɗanda suka kama. Wasu lokuta ma suna taka ciki na wanda suka kama a cikin watan Ramadan.”
Ya kuma yi magana kan yadda mutane ke tsoron ’yan siyasa fiye da ƙima.
Ya ce, “Ɗaya daga cikin masifa da wannan ƙarni yake fuskanta shi ne girmama mutane saboda tsoron abin da za su iya yi maka. Ku duba yadda gwamnonin jihohi ke tsoron Tinubu sama da yadda suke tsoron Allah.
“Idan kana APC ana ɗaukar ka kamar waliyyi. Idan kana adawa da ita, ana ɗaukar ka kamar shaiɗan, kuma za a iya ƙirƙiro maka sharri. Wane ne Tinubu? Ka yaudare mu. Kai mayaudari ne kuma maƙaryaci.”
Bayan dakatar da shi, Alƙali ya mayar da martani a shafinsa na Facebook, inda ya ce ya karɓi hukuncin da aka yanke a kansa.
Ya sanar da mabiyansa cewa Sheikh Jingir ba shugabansa na addini kaɗai ba ne, tamkar uba yake a wajensa.
Ya rubuta cewa, “Zuwa ga mabiyana, ’yan uwa da abokaina, ina roƙonku ku kwantar da hankalinku. Wannan abu ƙaddara ce.
“Ba zan wuce kwanakin da Allah Ya rubuta min na yi Tafsiri a Damaturu ba. Ku kasance masu biyayya da ladabi. Abin da Allah Ya ƙaddara shi ne mafi alheri gare mu.”
Daga baya, matasa da dama a kafafen sada zumunta sun soki dakatarwar da aka yi wa malamin.
Wani mai amfani da shafin Facebook, Yusuf Katagun, ya ce ƙungiyar Izala na daga cikin manyan matsalolin Arewa.
Ya rubuta cewa, “Izala na daga cikin manyan matsalolinmu a Arewa. Su ne suka dinga kira a kan a goyi bayan takarar Musulmi-Musulmi, suka kawo wannan mummunan shugabanci.”
Ya ƙara da cewa shugabannin ƙungiyar sun yi shiru a lokacin da jama’a ke buƙatar muryarsu fiye da kowane lokaci.
Sai dai wani mai suna Ahmad Usman El-nafaty ya ce abin da Alƙali ya yi wasan kwaikwayo ne kawai.
Ya ce, “Babu wani abin burgewa a abin da Alƙali ya faɗa. Wasan kwaikwayo ne kawai. Yana son ya ja hankalin mabiyansa ne. Yana mayar da Tafsiri kamar wasan barkwanci.”
Amma Ibraheem Ahmad ya ce dakatarwar ba daidai ba ce kuma ba ta dace da koyarwar Musulunci ba.
Ya ce, “Malamai su ne fata n ƙarshe ga talakawan Najeriya. Malamai da dama sun soki Tinubu amma ba a dakatar da su ba saboda ba su goyi bayan takarar Musulmi-Musulmi ba.
“Abin da Alƙali ya faɗa gaskiya ce mai ɗaci. Ya kamata malamai su ji tsoron Allah. Ku ne wakilan mutanen da ake zubar da jininsu.”
Shi kuwa Datti Assalfiy, ya ce sukar ’yan siyasa bai kamata ya zama dalilin dakatar da malami ba.
Ya ce, “’Yan siyasa ba su da addini. Shi ya sa yanzu malamin ya yi shiru.”
Har yanzu batun dakatarwar na ci gaba da jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link