Nasabar Annabi (SAW) Zuwa Ga Annabi Adam (AS)

[ad_1]

… ci gaba daga makon da ya gabata.

agana akan soyayyar Allah, magana ce mai girma har yazo a hadisi cewa, “fiyayyun bayin Allah, sune wadanda suke nunawa mutane son Allah da rahmarsa ba masu tsoratar da su ba, har mutum yaji ni meyasa ma aka halicce ni”.

Son Manzon Allah SAW dole ne. Allah ne ya sanya mana soyayyar, sai dai tawani tafi tawani, za kaga wani sabida ya hada da bi ko ibada, yana yinta cikin sauki sabida soyayyar, wannan itace soyayyar wajibi, to yanzu kowa shi yasan irin dabarar da zai yi don soyayyarsa ta karu.

Yazo a hadisi cewa, “Abubakar bai fiku ba, sai da Soyayyar Allah da ta Manzonsa,” sai son littafin Allah da son malamai wadanda za su nuna maka yadda zaka yi bautar Allah da rahmarsa. Magadan Manzon Allah a na’ibance suma sun shiga cikin wannan.

Na biyu daga cikin rabe-raben soyayya, itace soyayyar girmawa: wannan irin soyayya, itace ta son iyaye da girmamasu da kyautatawa da sonsu da yi musu biyayya ta inda bai saba wa Allah ba, bai hadu da son rai ko ziga ba, in ta hadu da wannan, ba za a yi musu biyayya ba, saidai a girmamasu.

Na uku, son shuwagabanni wadanda za su kiyaye mu, musanman masu damara kamar Soja, Dansanda, da dai sauransu. Duk mai son kasa ta cigaba sai ya so su, ya yi musu biyayya. Dole ne mutum yaso shugabanni kuma ya yi musu biyayya yadda tadace.

Na hudu, So na tausai, kamar ‘ya’yan da muka haifa, son da muke musu ba irin wanda muke yi wa iyayen mu ba ne, so ne na tausayi, zamu sasu a makaranta don a koya musu rayuwa ta addini da ta duniya. Shi son girmamawa, karami ne ke yi wa babba, shi kuma son tausayi, babba ne ke yi wa karami.

Na biyar, so na sha’awa, shi ne wanda muke yi wa matanmu, ba irin wanda muke yi wa mahaifiyarmu ko kannenmu ba, sai son mota da sha’war kaya masu kyau yazo a hadisi, “Allah mai kyau ne, yana son mai kyau”.

To shi son Manzon Allah, so ne na ibada da wajibi ba na sha’awa ba ko ganin dama ba.

Duk soyayyar nan da muka lissafo, tun daga ta girmamawa, da ta tausayi, da ta sha’awa, kowace in ka dube ta za kaga akwai abin da Dan’Adam yake yi dan ya sama wa kansa ita, kamar koyi da Annabi SAW gun kira zuwa ga addinisa, koyi da kyawawan halayensa, koyi da dabi’unsa, da koya wa kai soyayyar Annabi SAW, ba ta wasa ba.

An ruwaito hadisi daga Annabi SAW, ya tambayi Sayyadina Umar, “shin ko kasan ni waye?”, A zahiri, Sayyadina Umar yasan Annabi SAW, tun da har ya aura masa ‘ya, wannan sani ne ba na wasa ba, hakan na nufin cewa, soyayyar Annabi ba ta wasa ba ce, sabida haka, dole sai mun yi da gaske wurin koya wa kanmu son Annabi SAW.

An rawaito daga Annabi SAW, duk da wasu sun ce maganar ta Sayyadina Ali karramallahu wajhahu ce, amma shi ma ba wasa ba ne, “ku ladabtar da ‘ya’yanku a bisa son Annabinku, da son ‘yan gidansa, da karatun Kur’ani”. Shi ne duk irin zama da ake yi don fadan tarihin Annabi da koyar da sonsa, yadda magabata suka yi ba akida ba. Yabon Annabi SAW na kowane yare ne, manya da kanana duk sun yi don koya wa kai son Annabi SAW, “Mafi alkairinku, wanda yafi son Manzon Allah”.

Manzon Allah SAW, ubangijinsa ya yi masa komai na alkairi kamar yadda mu al’ummmarsa muka samu alkairi. Allah ya ba shi iyaye masu alkairi, kuma ana alfahari da iyaye, kamar ince, ni ne dan gidan wane, da wane, nasabar Annabi SAW, ta kai har kan Annabi adamu AS, kuma dukkansu masu alkairi ne.

Allah ya bashi ‘ya’ya masu alkairi, kowa yana alfahari da ‘ya’ya masu alkairi, za ka ji ana cewa, Dana wane ne da matsayinsa; Allah ya bashi surukai masu girma, kowa yana alfahari da surukansa. Manzon Allah SAW, sunan mahaifinsa Abdullahi, sunan kakansa Abdul-muddalibi, dan Hashim, dan Abdulmanafi, dan Kusaiyu da ake ce masa Kuraishu karami, sabida yana daga wanda ya hada kuraishawa, shi kuma dan Murratu, dan Ka’abu, dan Lu’ayyu, dan Galibu, dan Fihru, dan Maliku, dan Nadru, ana ce masa Kuraishu na tsakiya, kila shi ne Kuraishun ma gaba daya, dan Kinanata, dan Kuzaimata, dan Mudrikata, dan Ilyasi, ana ce masa ilyasu dan Mudar, dan Nizaru, dan Ma’addi, dan Adnanu.

An rawaito Manzon Allah SAW dakansa yana fadan iyayensa zuwa kan Adnanu, kuma an tabbatar, jikan Annabi Ibrahim As ne, duk da cewa, akwai sabani acikin jerin kakanninsa.

Daga kan Annabi SAW zuwa kan Adnan, akwai kaka 20, daga Annabi SAW zuwa kan Annabi Ibrahim AS, akwai kaka 66, Adnan, jikan Annabi Isma’ilu ne, jikan Annabi Ibrahim AS. akwai sabani akan sunayensu, sabida tsakanin mutuwar Annabi Isma’ilu AS zuwa kan haihuwar Annabi SAW, tsakaninsu akwai shekara 2609.

To iKon Allah akwai wani bawan Allah da yayi littafi mai suna, “UMDATUT-DALIBI FIN NASABI ABI DALIBI”, Littafi;ne dadadde da ya kai Shekara 1000 da yin wannan littafin, ya kawo cewa, an samu da rubutun Annabi Baruku, Almajirin Annabi Irmiya wanda muke cema Armayau cewa, Annabi Baruku dan Irmiya wanda ya yi zamani da Mu’addu, ya kawo salsalar Annabi har zuwa kan Isma’ilu, da cewa Adnanu dan Adada, dan Hamaiza’i, dan Hamaisa’a, dan Salaman, dan Audu, dan Lawari, dan Shuki, dan Nu’amani, dan Kasdani, dan Hazabi, dan Kasdalani, dan Tadalabi, dan Dahbi, dan Bahsha, dan Ma’ajaki, dan Gafani, dan Afadi, dan Ifda’i, dan Hamdani, dan Yashnani, dan Batrani, dan Amrani, dan Malhani Ra’awani, dan Akani, dan Dandaishani, dan Asari, dan Mayadi, dan Samini, dan Maƙsari, dan Fahisu, can Raziku, dan Shama, dan Yazzi, dan Safa, dan Tami, dan Kaizaru, dan Isma’ilu, dan Ibrahim.

Da wannan ya zama, kaka 37 in aka dora 37 kan 20, yazama kaka 57 zuwa Annabi Ibrahim.

Nasabar Annabi Ibrahim zuwa Annabi Adam: Annabi Ibrahim dan taraku, dan Nahuru, dan Sharuhu, dan Falugu, dan Abiru, dan Shaluku, dan Arfakazu, dan Samu, dan Nuhu (mai jirgin ruwa). An samu kaka 9, in aka doa kan 57, ya zama 66. Annabi Nuhu dan Mashkadu, dan Lamku, dan Matushalaku, dan Akhnuku (Annabi Idrisu), dan Yarizu, dan Mahla’ilu, dan Kainanu, dan Sha’anusu, dan Shisu, dan Annabi Adamu As. An kara samun kaka 10, in aka dora kan 66, ya zama 76. Wannan shi ne salasalar Annabi SAW da duk Ahlussuna suka hadu akanta.

Tarihin Annabi SAW a takaice: An haifi Annabi SAW 20 ga Afrilun 521 Miladiyya, Allah ya aikoshi 10 ga August shekara ta 610 Miladiyya, ya sauka a Madina 20 ga Septemba, shekara ta 622 Miladiyya, ya yi yakin Badar 13 ga maris, shekara ta 623 Miladiyya, ya yi Fathu Makkata, 10 ga Janairun shekarar 630, ya yi Hajjin ban-kwana a maris, shekara ta 632 miladiyya, ya koma ga Allah a watan Yuni, shekara ta 632 miladiyya SAW.

Ga masu zuwa da yara wuraren taron Ibada, yana da kyau, mutane su fahimci cewa, kowanne mutane suna da tsarin al’adarsu yadda suke abubuwan su, ainihin maulidi a masallaci ake yi kamar yadda yazo a hadisin Abdullahi bin Abbas, yananan a Nujumul Huda Hadisi ne ingatacce da Annabi SAW ya fito, Sahabbai suna zaune suna fadin tarihin annabawa cewa, Annabi wane, Allah ya yi masa kaza da kaza, Annabi SAW yana tsaye amma basu san yana tsaye yana jinsu ba, sai yace musu, naji abin da kuke fada, duk haka ne amma ku saurara, ni kuma nine kaza da kaza, haka ya rika fadin darajarsa don godiya ga Allah. Haka ake yi, a Kano da sauran garuruwa.

An fara yin hakan ne a makarantun islamiyya, wanda shehunan mu suka fara tun daga wajen 1950.

Babbar Mu’ajizar Annabi SAW, itace Kur’ani, ba yanke haddi da tsanani ba, wanda ya yi nuni da mu rika yin soyayya wadda ita za ta kaimu ga shiga aljanna.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *