An kashe jami’an tsaro 11 a Kebbi

[ad_1]



Aƙalla jami’an tsaron Najeriya 11 ‘yan bindiga suka kashe a wani kwantan ɓauna da suka yi masu a Giron Masa a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.

An kai harin ne  a ranar Talata da daddare da ya gabata in da jami’an suke sintiri a yanki.

Jami’an soja sun yi ƙoƙarin kare yankin amma aka yi masu kwantan ɓauna.

Sojoji da ‘yan sanda sun rasa rayukansu da manyan motocin yaƙi guda biyu aka ƙona.

Gwamnan Jihar Kebbi,  Nasir Idris ya ziyarci wurin da kuma asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke birnin Kebbi domin duba lafiyar waɗanda suka jikkata.

Gwamnan ya yi tir da rashin hankalin ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta kula da mutanen da suka samu rauni.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *