Ba Lallai Ba Ne, Brazil Ta Iya Lashe Gasar Kofin Duniya Na Bana Ba – Vinicius
[ad_1]
Ɗan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma tawagar kwallon kafa ta kasar Brazil Vinicius Junior ya bayyana cewa kasar Brazil bata cikin kasashen da ake yiwa kallon wadanda zasu iya lashe gasar kofin Duniya na shekarar 2026 ba.
Da yake magana a wani taron manema labarai kafin wasan sada zumunci tsakanin kasar Brazil da Faransa, inda Vinicius din yace sakamakon wasanni na baya bayan nan da kasar ta buga yasa ba a kallonsu a matsayin wadanda zasu iya lashe gasar, “Ina ganin bamu cikin wadanda ake hasashen zasuyi nasara duba da sakamakon wasanninmu na baya bayan nan” inji Vinicius.
“Amma kuma darajar rigar da muke dante da ita zai kara mana kaimi wajen gani. mun samar da abinda ake bukata yayin buga gasar, abin da kawai muke bukata shi ne goyon baya daga magoya baya, za mu yi duk abin da za mu iya domin dawo da martabar kasar Brazil a fagen kwallon kafa” Vinicius ya kara da cewa.
Brazil da Faransa za su fafata a filin wasa na Gillette da ke birnin Massachusetts a yau Alhamis a wani wasa da zai iya gwada yadda kasashen ke shirye shiryen buga gasar cin kofin Duniya da za a buga a. kasashen Amurka, Mexico da kasar Canada a watan Yuni na wannan shekarar ta 2026 da muke ciki.
[ad_2]
Source link