Yadda Ake Soya Gurasa Cikin Kwai
[ad_1]
Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da Sallah, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan makon wanda shi ne mako na farko bayan Sallah Allah ya maimaita mana, a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake soya Gurasa cikin Kwai:
Abubuwan da za a tanada:
Gurasa, Kwai, Tattasai, Koran wake, Karas, Albasa, Magi, Gishiri, Kori.
Yadda ake hadawa:
Idan kika samo Gurasa sai ki samu ruwan zafi ki dan tsutssumata a ciki kina cirewa saboda ta yi laushi, sai ki samu kwano ki fasa Kwai a ciki daidai yadda zai ishe ki, sannan sai ki kawo Tattasai ko Attarihu duk wanda kike so wanda dama kin wanke shi sannan ki jajjaga shi ki zuba, sai ki kawo yankakkiyar Albasa ki zuba sai ki kawo Karas da koran wake wanda dama kin yanka su ki zuba, sannan ki zuba Magi, Gishiri, Kori.
Sai ki hada ki gauraya ya hade gaba daya.
Sannan ki dora Mai idan ya yi za fi ki zuba Albasa, sai ki rika dauko wannan Gurasar da kika sa a ruwan zafi kina sakawa a cikin Kwan kamar yadda ake Doya da Kwai, sai ki rika tsamewa kina sakawa a man kina soyawa kamar yadda ake soya Doya da Kwai. Tana kyau ga dadi. A ci dadi lafiya.
[ad_2]
Source link