Babu Umarnin Kotu Da Ya Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta A Abuja – Mrakpor


Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Delta, Dakta Peter Mrakpor, ya bayyana cewa babu wani umarnin kotu da ya hana jam’iyyar gudanar da babban taronta na ƙasa da aka shirya yi a ranakun 29 zuwa 30 ga Maris, 2026, a Abuja.

Mrakpor, wanda Babban Lauyan Nijeriya (SAN) ne, ya yi wannan bayani ne yayin da ake ta yaɗa jita-jita da rade-radin cewa za a iya dakatar da taron saboda ƙalubalen shari’a.

  • Hanyoyin Magance Warin Gashin Kai Ga Mata
  • Gwamnan Zamfara Zai Halarci Taron Horaswa Na Dabarun Shugabanci A Jami’ar Coventry Ta Ƙasar Birtaniya

Ya yi watsi da irin waɗannan zarge-zarge, yana mai cewa, jita-jita ce kawai.

A cewarsa, dukkan shirye-shiryen da ake bukata domin gudanar da taron suna nan daram, yana jaddada cewa jam’iyyar a shirye take ta ci gaba da gudanar da taron kamar yadda aka tsara ba tare da wata matsalar doka ba.

Shugaban PDP na Delta ya kuma bukaci duk wakilan jihar da su yi watsi da abin da ya kira “masu yada jita-jita” tare da tabbatar da cikakken halartarsu a taron da za a yi a Abuja.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *