Babban taron PDP mataki ne na tunkarar zaɓen 2027 — Saraki
[ad_1]
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce babban taron jam’iyyar PDP da ke tafe shi ne babbar damar da jam’iyyar ke da ita domin fafatawa a zaɓen 2027.
Ya shaida wa Aminiya cewa yana goyon bayan taron gaba ɗaya domin bai wa ’yan jam’iyya damar tsayawa takara.
Saraki ya ce idan taron ya gudana yadda ya kamata, duk da ƙarar da ɓangaren jagorancin Tanimu Turaki ya shigar, PDP za ta iya tsara kanta tare da fitar da ’yan takara.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata jam’iyyar ta mayar da hankali kan manufofinta, ba son rai ko rikicin cikin gida ba, yana mai cewa matasa da dama na son tsayawa takara a jami’yyar PDP.
Ya ƙara da cewa ba ya goyon bayan wani ɓangare na jam’iyyar, illa dai duk wanda ke ƙoƙarin tabbatar da PDP ta shiga zaɓen 2027.
Saraki ya kuma ce PDP na da damar samun nasara, musamman ganin cewa jam’iyyar APC na iya fuskantar matsaloli cikin gida.
Ya musanta zargin cewa yana aiki tare da Nyesom Wike domin taimaka wa APC, tare da cewa ba shi da shirin barin PDP.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link