NAHCON Ta Jaddada Ƙudirinta Na Kammala Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 A Kan Lokaci
[ad_1]
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sake jaddada aniyar Hukumar na yin shiri tun da wuri, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi da bin ƙa’idoji da tsare-tsare, domin tabbatar da gudanar da Hajjin 2026 cikin tsari da nasara.
Mai taimaka wa Shugaban NAHCON kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Mu’azu, ya bayyana cewa Farfesa Usman ya ce Hukumar na aiki ne bisa tsarin manufofin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, da kuma Shirin “Renewed Hope”, wanda ke bai wa walwala da jin daɗin ibadar alhazan Nijeriya muhimmanci. Ya ce NAHCON na aiki ne a ƙarƙashin kulawar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda ke jaddada kammala muhimman shirye-shiryen Hajji a kan lokaci.
- Lokaci Ya Yi Na Kawo Karshen Kashe-kashen Da Ake Yi A Kano
- Yadda Ake Hada Dilka Na Amare
Shugaban Hukumar ya nuna cewa an bai wa tanadar masaukin alhazan jihohi a Makkah muhimmanci matuƙa, tare da bin ƙa’idoji da jadawalin da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
A daidai wannan lokaci, Farfesa Usman ya amince da tura tawagar manyan jami’ai zuwa Ƙasar Saudiyya nan take. Tawagar, wadda Shugaban zai jagoranta, za ta duba tare da kammala karɓar dukkan shirye-shiryen masauki da suka rage a Makkah, domin kauce wa jinkiri da tabbatar da bin dokokin Saudiyya.
’Yan tawagar sun haɗa da:
1. Farfesa Abubakar A. Yagawal – Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Yaɗa Bayanai da Ayyukan Laburare (PRSILS)
2. Sheikh Muhammad Bin Uthman – Mamba, Yankin Arewa maso Yamma
3. Dr. Tajudeen Oladejo – Mamba, Yankin Kudu maso Yamma
4. Hajiya Aishat Obi Ahmed – Mamba, Yankin Kudu maso Gabas
5. Dr. Mustapha Mohammed Ali – Sakatare na Hukumar
An umarci tawagar da ta kammala dukkan shirye-shiryen masauki tare da miƙa cikakken rahoto ga Hukumar nan take bayan kammala aikin.
Sai dai Shugaban Hukumar zai ci gaba da zama a Nijeriya domin tarɓar Ministan Hajji da Umrah na Ƙasar Saudiyya, Dr. Tawfiq Al-Rabiah, wanda ake sa ran zai kai ziyara Nijeriya a wannan watan, tare da ci gaba da sa ido kan ayyukan Hukumar.
Farfesa Usman ya ƙara da cewa NAHCON ta ƙarfafa tsare-tsaren cikin-gida na shugabanci, haɗin kai da sa-ido domin tabbatar da gaskiya, bin doka da ingantaccen tsarin aiwatarwa. Wannan ya haɗa da ci gaba da tuntuba da mambobin Hukumar, manyan jami’ai, masu samar da ayyuka da kuma hukumomin Saudiyya, domin bin ƙa’idojin da aka gindaya.
Ya jaddada cewa dukkan matakan Hukumar na fitowa ne bisa ikon doka da aka ba ta a matsayin hukumar da ke kula da aikin Hajji a Nijeriya. Ya ce yanke hukunci a NAHCON na tsari ne na hukuma, ana yin sa bisa ƙa’ida da haɗin kai, ba na mutum ɗaya ba, tare da kare muradun alhazan Nijeriya da ƙarfafa dangantakar Nijeriya da Ƙasar Saudiyya.
A ƙarshe, Shugaban ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki da alhazan da ke shirin tafiya cewa NAHCON na da ƙudirin gudanar da Hajjin 2026 cikin sauƙi ba tare da tangarda ba, ta hanyar ƙarfafa tsare-tsare, inganta shiri da ɗa’a, da bunƙasa ƙwarewa bisa ƙa’idojin da duniya ta amince da su. Ya kuma ce Hukumar za ta ci gaba da fitar da bayanai na hukuma ta kafafen sadarwarta yayin da shirye-shiryen Hajjin 2026 ke gudana.
[ad_2]
Source link