Hare-haren Isra’ila Ta Sama Ya Kashe Falasɗinawa 11 A Gaza

[ad_1]

Hare-haren sama na Isra’ila sun kashe Falasdinawa 11 a Zirin Gaza a ranar Asabar, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin, ciki har da mutanen da ke fakewa a cikin tanti.

Munir al-Barsh, babban daraktan ma’aikatar, wanda ke aiki a karkashin ikon Hamas, ya shaida wa kamfanin AFP cewa, mutane 11 sun mutu sannan wasu 20 sun jikkata “sakamakon hare-haren da Isma’ila ta kai kan fararen hula a cikin tanti da wani gida”.

Barsh ya ce, wadanda suka jikkata an kai su a asibitoci a birnin Gaza da ke arewa da kuma Khan Yunis a kudu.

Isra’ila “ta ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta a daidai lokacin da ake fama da karancin kayayyakin kiwon lafiya, magunguna da kayan aikin likita,” in ji Barsh.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *