Mutum 12 sun rasu a hatsarin mota a Filato da Kogi

[ad_1]



Aƙalla mutum 12 ne suka rasu a hatsarin mota daban-daban da suka auku a Jihohin Filato da Kogi.

A Jihar Filato, fasinjoji 10 ne suka rasu a ranar Talata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a wani shingen binciken sojoji da ke kan hanyar Jos zuwa Bauchi, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Mutane da dama kuma sun jikkata.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Kasa (FRSC) ta ce hatsarin ya faru da misalin karfe 12 na dare.

Motoci huɗu ne suka yi hatsari, ciki har da tirela guda biyu da kuma ƙananan motoci guda biyu.

Mutum 19 ne ke cikin motocin, maza 17 da mata biyu.

Maza 10 manya sun mutu nan take, bayan faruwar hatsarin.

Jami’an FRSC tare da ’yan sanda, jami’an gwamnati da mazauna yankin sun taimaka wajen ceto waɗanda abin ya shafa.

An kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Miya Barkate, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) da kuma Asibitin Ƙwararru na Jihar Filato.

An kai gawawwaki takwas zuwa ɗakin ajiye gawa na Asibitin Ƙwararru na Filato da Jami’ar Bingham, yayin da jami’an ƙungiyar direbobi (NURTW) suka karɓi gawar mutum biyu domin yi musu jana’iza.

FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa gudu da ganganci ne suka haddasa hatsarin.

Hukumar ta shawarci matafiya da su guji tafiya cikin dare tare da rage gudu, domin kiyaye lafiyarsu.

Wannan hatsarin ya faru ne kwanaki 12 bayan da ɗaliban Jami’ar Jos guda tara suka rasu a wani hatsari da ya faru a hanyar Zariya a Jos.

A Jihar Kogi kuwa, mutum biyu suka rasu yayin da wasu 12 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a yankin Osara, da ke Ƙaramar Hukumar Adavi.

FRSC ta ce mutum huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali amma an garzaya da su asibiti.

Hatsarin ya shafi wata bas mai ɗaukar fasinjoji 18 ƙirar Toyota Hiace da kuma babbar mota.

Bas ɗin ta taso ne daga Kano kuma tana kan hanyarta na zuwa Auchi da Benin, lokacin da hatsarin ya faru tsakanin karfe 7 zuwa 8 na safiyar ranar Talata.

FRSC, ta danganta hatsarin da gudun wuce ƙima da ƙetare mota ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar ta kuma buƙaci direbobi da su kiyaye dokokin hanya, musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *