Sojojin sun dakile yunƙurin garkuwa da matafiya a Binuwai, sun ceto fasinjoji 18

[ad_1]



Sojojin rundunar tsaro tOperation Whirl Stroke rana dakile wani yunƙurin garkuwa da mutane a kan hanyar Otukpo–Enugu da ke Jihar Binuwai, inda suka ceto fasinjoji daga motocin haya biyu.

A cewar sojojin, lamarin da tilasta wa ’yan bindiga guduwa da kafarsu.

Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 10 na dare, bayan samun kiran gaggawa, inda sojojin da ke sintiri suka garzaya zuwa yankin Amoda a Karamar Hukumar Ohimini.

Kakakin rundunar, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, a cikin wata sanarwa ya ce, ’yan bindiga dauke da makamai sun fito daga daji, sannan suka mamaye wani shingen bincike na wucin gadi, suka tsayar da motoci biyu masu ɗauke da fasinjoji 18 da suka taso daga Jos zuwa Ibadan.

Sai dai zuwan sojojin Operation Whirl Stroke cikin gaggawa ya haifar da musayar wuta, wanda ya tilasta wa ’yan bindiga barin fasinjojin da suka kama tare da guduwa cikin daji.

Ya ce da farko an kubutar da fasinjoji 15 inda aka mika su ga ofishin ’yan sanda na Otukpo.

Laftanar Ahmad ya ce dukkan mutanen da aka ceto yanzu suna hannun ’yan sanda a Otukpo, yayin da ake ci gaba da bincike don gano ragowar fasinjojin.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa gaggawar da suka yi da kuma nuna kwarewarsu.

Ya tabbatar da kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da ci gaba da kai hare-hare, yin sintiri bisa bayanan sirri, da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin hana ’yan ta’adda samun mafaka a yankin.

Janar Gara ya kuma aika da sakon gaisuwar Kirsimeti da bikin ƙarshe na shekara ga mabiya addinin Kirista a jihohin Binuwai, Nasarawa da Taraba, inda ya yi addu’ar samun zaman lafiya da rahamar Allah.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *