Za a hukunta waɗanda suka ƙona shingen itatuwa — Gwamnan Sakkwato
[ad_1]
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya umurci jami’an tsaro a ƙaramar hukumar Wurno da su kama waɗanda ke da alhakin ƙona shingen itatuwa da aka kafa domin daƙile gabatowar hamada a yankin.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin ƙaddamar da sayar da takin zamani akan farashi mai rahusa domin noman rani a Wurno.
Ya bayyana matuƙar baƙin ciki kan lalata shingen itatuwan, inda ya bayyana wannan aiki a matsayin mugunta da rashin imani da kuma abin da kan iya lalata muhalli.
“Ina mamakin yadda wani zai iya ƙona shingen itatuwan da aka dasa domin kare muhallinmu daga mamayar hamada, duk da gangamin wayar da kai da aka yi game da hana sare itatuwa barkatai,” in ji Gwamnan cikin takaici.
“Ba a yarda a sare itatuwa barkatai a kowane hali ba, kuma duk wanda aka kama yana aikata hakan zai fuskanci hukuncin doka,” in ji shi.
Gwamna Ahmed Aliyu ya jaddada cewa, dole ne jami’an tsaro a yankin su gano tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aiki, yana mai nanata cewa ya zama dole a hukunta su domin ya zama izina ga wasu.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnati, Sakkwato, Abubakar Bawa, ya fitar.
Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin Jihar na kashe maƙudan kuɗaɗe a duk shekara wajen samarwa da kula da dubban tsirren itatuwa, waɗanda ake rabawa yankunan da ke fuskantar barazanar mamayar hamada a faɗin jihar.
Gwamnan ya umurci Shugabannin Ƙananan Hukumomi a yankunan da ke fuskantar mamayar hamada da su tabbatar da kulawa da tsare shingen itatuwan da ke ƙarƙashin ikonsu.

Wuraren da aka kona.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link