JIBWIS Ta Aurar Da Mahaddata Da Makaranta Ƙur’ani Mata Marayu 30
[ad_1]
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Abuja ta gudanar da taron aurar da mata marayu mahaddata Ƙur’ani 10 da makaranta 20 ranar Laraba a Shalkwatar kungiyar dake Abuja.
Shugaban Kungiyar na Kasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, shi ya jagoranci ɗaurin auren. Da yake jawabi yayin gudanar da taron, Shehun malamin, ya ja hankalin al’ummar Musulmi kan muhimmacin kula da marayu da irin falal da ladan dake tattare da faranta wa marayu, inda ya ba da misali da yadda shugaban halitta Annabi Muhammad SAW, ya taso yana maraya cikin rashin uwa da uba, wanda ya ce Allah ya yi hakan ne domin mutane su sani cewa, kowa zai iya tsintar kansa a wannan matsayi.
- Yadda Fasahar Sin Ke Agaza Wa Samun Wadataccen Hatsi A Afirka
- Yanzu- Yanzu An Sako Masu Ibadar da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
Ya ce, “Manzon Allah (SAW) yana cewa duk wanda ya kula da maraya, to zai zauna kusa da ni a aljanna. Sannan a wani Nassin manzon Allah yana cewa, taimako da kuke samu duk Allah yana baku ne saboda tausaya wa masu raunin da suke cikinku.”
Sannan ya ce, Allah kadai shi ne ya san wane ne zai zama maraya. Sai ya bar mu da darasi da aya don mu tausaya wa maraya. Ya ja hankalin masu rike da marayu da su guji muzguna musu da cinye musu hakki.
A jawabin da ya yi ga manema labarai a yayin taron, mataimakin shugaban kwamitin marayu na kasa, sannan shugaban kwamitin marayu na kungiyar reshen Abuja, Abdullahi Abdulmalik Digi, cewa ya yi, wannan taro na aurar da mata marayu makaranta Alƙur’ani, akan yi shi ne sau daya a shekara, inda ake tattara marayu mata sannan a ɗauki nauyin aurar da su a ɓangarori biyu: na farko, waɗanda suka haddace Ƙur’ani, ɗaya ɓangaren kuma, waɗanda basu haddace ba.
Ana tantance mahaddata ne ta hanyar shirya Musabaka domin tabbatar da ingancin haddarsu, ba tare da la’akari da an san daga inda yarinya ta fito ko iyayenta ba, domin suna ba da cigiya ne sai a kawo su a tantance.
Maryam Hamza Imam, na ɗaya daga cikin marayu matan da aka aurar, ta bayyana wa LEADERSHIP Hausa irin farin cikinta da godiya ga wannan Kungiya ta JIBWIS da addu’ar Allah ya saka musu da alheri.
[ad_2]
Source link