Sufeto-Janar Na ‘Yansandan Nijeriya Kayode Egbetokun, Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa
[ad_1]
Sufeto-Janar na ‘Yansandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Kawo yanzu ba a bayyana dalilin murabus ɗinsa ba.
- Haƙƙin Ɗan’adam Na Fuskantar Mummunar Barazana A Duniya – Guterres
- Mutum 1 Ya Rasu Yayin Da Sojoji Suka Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Ƙauyukan Benue
Sai dai majiyoyi daga rundunar ‘yansandan sun tabbatar cewa an sanar da manyan jami’ai a ranar Litinin game da murabus ɗinsa.
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi a watan Yunin 2023 a matsayin Sufeto-Janar na 22.
Bayan ya kai shekarun ritaya a watan Satumban 2024, an ƙara masa wa’adin shekaru huɗu bayan gyaran dokar ‘yansanda.
Har zuwa yanzu, Hedikwatar ‘Yansanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan dalilin murabus ɗinsa ba.
Karin bayani na tafe…
[ad_2]
Source link