Binciken CGTN: Gasar Wasannin Olympics Ta Hunturu Ta Milan-Cortina Ta 2026 Ta Kunna Haske Fiye Da Na Kankara Da Dusarta

[ad_1]

Gasar Wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milan-Cortina ta shekarar 2026 ta kimtsa tsaf wajen tsunduma cikin “zamanin Italiya,” inda za su sake jawo hankalin duniya zuwa fagen wasannin hunturu da ke samun bunkasa. Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta gudanar a tsakanin masu amfani da intanet na duniya ya nuna cewa kashi 61.2% na masu bayyana ra’ayoyin, sun yi amannar dabi’un wasannin Olympics na iya kara hada kan al’ummar duniya, tare da bayyana fatan cewa gasar za ta zama muhimmin dandali na karfafa tattaunawa, cudanya, da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe.

Gasar Wasannin Olympics ta Hunturu a wannan shekara ta mayar da hankali kan manufofin kare muhalli, inda aka yi tsari mai dorewa da kayatarwa ga yanayin fitilar wuta, da lambobin yabo, da gina wuraren fafatawa. Binciken ya nuna cewa kashi 58.1% na wadanda suka bayyana ra’ayoyin sun yi amannar wannan mataki amsa ce mai kyau ga neman ci gaba mara gurbata muhalli da rage yawan fitar da hayaki mai guba.

Bugu da kari, kashi 75.2% na masu bayyana ra’ayoyin sun amince cewa gyare-gyare da gina tituna, layukan dogo, da wuraren fafata wasannin wadanda birane masu masaukin wasannin suka aiwatar domin nuna goyon baya ga gasar, sun ba da wata muhimmiyar dama ta inganta dukkanin ababen more rayuwa masu nasaba da wasannin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *