AU ta yi martani kan harin da ya kashe mutum 170 a Najeriya
[ad_1]
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana ta’aziyya a ranar Alhamis tare da yin Allah wadai da wani harin ta’addanci wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170 a Najeriya.
Shugaban Hukumar AU, Mahmoud Ali Youssouf ya kira harin a matsayin “mummunan aiki da rashin imani,” na take haƙƙin dan Adam da kuma wani hari “wanda ba za a yarda da shi ba” kan zaman lafiya da tsaro, a cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba.
Youssouf ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa tare da bayyana “cikakken goyon baya” ga gwamnatin Nijeriya da hukumomin Jihar Kwara.
Ƙungiyar AU ta sake jaddada ƙudirinta na tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya na ƙarfafa zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.
Ita ma Jamhuriyar Benin ta bayyana “ta’aziyyarta ta musamman” ga iyalan waɗanda abin ya shafa, al’ummar Najeriya da kuma gwamnati.
Ta sake jaddada goyon bayanta ga Abuja wajen yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, inda ta nuna muhimmancin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Tuni dai Gwamnatin Kwara ta tabbatar da cewa an binne mutum 75 a kabarin bai-ɗaya a ranar Laraba, amma ɗan majalisar yankin Saidu Baba Ahmed ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa an gano gawawwaki 170, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.
“Bayanan da ke hannuna sun nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai 170. Don haka, mutanenmu har yanzu suna cikin daji suna neman ƙarin gawawwaki. An sace mata 35. Waɗanda suka tsira su ma suna neman mafaka a cikin daji,” in ji shi.
Bayanai sun ce harin da aka kai a yammacin Talata a ƙauyen Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiaman Jihar Kwara ya zo ne bayan Sojin Najeriya sun kai hari tare da ragargaza abin da su ka kira maɓoyar ’yan ta’adda.
Jihar Kwara, musamman al’ummomin da ke maƙwabtaka da dazuzzuka, a cikin ’yan watannin nan ta fuskanci ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa mai alaƙa da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke tserewa daga matsin lambar soja a jihohin da ke maƙwabtaka da ita a yankunan arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link