Mutane 6 Sun Rasu, 23 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kan Hanyar Legas–Ibadan
[ad_1]
Mutane shida sun rasu yayin da wasu 23 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a kan babbar hanyar Legass zuwa Ibadan, kusa da Four Square Camp.
Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta ce hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11:27 na safiyar ranar Litinin, kuma wata babbar mota ce kaɗai ta yi hatsarin.
- Ƙofor APC A Buɗe Take Ga Kwankwaso — Yilwatda
- Ƴansandan Abuja Sun Nemi NLC Ta Dakatar Da Zanga-zangar Da Ta Shirya Gobe
Kakakin FRSC, Odunsin Afolabi, ya ce jimillar mutane 29 ne ke cikin motar a lokacin da hatsarin ya faru.
Ya bayyana cewa gudun wuce gona da iri da gajiya da direba ya yi ne suka haddasa hatsarin, wanda ya sa direban ya kasa sarrafa motar.
An kai waɗanda suka jikkata da gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa Asibitin Oreoluwa, GOFAMINT Camp, Ogunmakin, da Asibitin Victory, Ogere.
FRSC ta shawarci direbobi da su guji gudu da sauri, suke hutawa kafin yin tuƙi, kuma su riƙa duba lafiyar motocinsu akai-akai.
[ad_2]
Source link